Gobe ne fa: Abubuwa 7 da ya kamata a lura da su game da taron gangamin APC na kasa

Gobe ne fa: Abubuwa 7 da ya kamata a lura da su game da taron gangamin APC na kasa

  • Bayan dagewa da kai ruwa rana, yanzu dai an shirya komai don gudanar taron gangamin jam'iyyar APC na kasa
  • Taron wanda ake sa ran zai gudana a ranar Asabar 26 ga watan Maris, zai gudana ne a dandalin Eagle Square dake Abuja
  • Akalla mutane 169 ne suka sayi fom din tsayawa takara a mukamai daban-daban sama da 22 a Kwamitin Ayyuka na Kasa (NWC) na APC

Ana ci gaba da gudanar shirye-shiryen don taron gangamin jam'iyyar APC na kasa da aka dade ana jira.

Tun da farko an tsara yin taron a ranar 26 ga watan Fabrairu, amma aka samu tsaiko shugabancin jam'iyyar mai mulki a Najeriya, ta dage shi zuwa ranar 26 ga Maris a matsayin saboda wasu matsaloli da suka gindayo.

Kara karanta wannan

Mu ya mu: ‘Yan takarar shugaban kasa na PDP sun gana don zaban daya kwakkwara

An nada kwamitoci goma sha tara da za su kula da tsarukan da suka dace don gudanar da taron da za a yi a dandalin Eagle Square, Abuja.

Taron gangamin APC: Abubuwa 7 game da taron APC
Abubuwa 7 da ya kamata a lura da su cikin gaggawa game da taron jam'iyyar APC na kasa na ranar 26 ga Maris | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Gabanin taron na jam’iyya mai mulki na gobe, Legit.ng ta hado muhimman abubuwa guda 7 game da ayyukan taron gangamin kamar yadda jaridar The Nation da Premium Times suka ruwaito.

1. Akalla mutane 169 ne suka sayi fom din tsayawa takara a mukamai daban-daban a kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na kasa (NWC).

2. Taron dai ana sa ran zai samu halartar wakilai kusan 4,000 daga Jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT).

3. Wasu mutane bakwai da suka nuna sha’awar tsayawa takarar shugabancin jam'iyyar na kasa sun samu damar sayen fom din takararsu wanda ya kai farashin kudi Naira miliyan 20 kuma tuni an tantance su.

Kara karanta wannan

Taron gangamin APC: APC ta fitar da jerin abubuwa 29 da za su gudana a taron gangaminta

4. Jam’iyyar APC ta hana masu rike da mukaman siyasa kada kuri’a a babban taronta na kasa sakamakon cece-kucen da ya biyo baya game da sashe na 84 (12) na dokar zabe, 2022. An ba su damar halartar taron ne kawai inda su zama masu sa ido.

5. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana ra’ayinsa na ganin an samar da daidaito da yarjewa tsakanin 'yan takara, kuma rahotanni sun ce ya zabi tsohon gwamnan Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu.

Sai dai wasu masu ruwa da tsaki a APC sun yi watsi da shawarin Buhari na zaban Adamu a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa da Nnamani a matsayin mataimakinsa (Kudu) bisa abin da suka bayyana a matsayin alamun mayar da APC hannun ‘yan PDP na asali.

6. Jam’iyyar APC ta sanar da jama’a cewa za a rufe dukkan hanyoyin zuwa dandalin Eagle Square da ke Abuja domin gudanar da taronta na gangamin na kasa da aka shirya yi a gobe Asabar.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Jiga-jigan sanatocin APC za su gana da shugaba Buhari a yau Alhamis

7. Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan jama'a na na taron ya fitar da jadawalin abubuwan da za su faro a taron.

Abdullahi Adamu mukayi ittifakin ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC, Gwamna Sule

A wani labarin, gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya tabbatar da cewa jam'iyyar All Progressives Congress ta zabi tsohon gwamna, Abdullahi Adamu, matsayin wanda za'a zaba sabon shugabanta.

Sule ya bayyana hakan da yammacin Juma'a yayin hira a shirin Politics Today na tashar ChannelsTV.

Gwamnan wanda yayi magana kan shirye-shiryen da jam'iyyar ke yiwa taron gangamin gobe Asabar, ya ce dokar zabe ta amince da hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel