Taron gangamin APC: APC ta fitar da jerin abubuwa 29 da za su gudana a taron gangaminta

Taron gangamin APC: APC ta fitar da jerin abubuwa 29 da za su gudana a taron gangaminta

 • Jam'iyyar APC ta shirya gudanar da taronta na gangami a ranar Asabar 26 ga watan Maris, ta bayyana shirinta
 • Daga jadawalin da jam'iyyar ta fitar, an bayyana lokutan da shugabanni da jiga-jigan jam'iyyar za su iso
 • Jerin ya bayyana abubuwa sama 29 da za su faru a taron na gangami da jam'iyyar APC ta tsara a Abuja

Abuja - Jaridar Leadership ta rahoto cewa, gabanin taron gangamin jam’iyyar APC mai mulki a ranar 26 ga Maris, kwamitin yada labarai na taron ya fitar da wani jadawalin shirin gudanar da taron jam’iyyar na ranar Asabar mai zuwa.

Shugaban kwamitin yada labarai na babban taron jam’iyyar APC na kasa na 2022, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ne ya fitar da jadawalin taron da aka shirya gudanarwa a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Fayemi ya yi watsi da batun goyon bayan yan takarar da Buhari ke so

Taron gangamin APC na zuwa nan kusa
Jam'iyyar APC ta fitar da shirin gudanar da babban taron kasa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Jerin abubuwan da za a yi a taron gangamin APC na kasa

A kasa mun kawo muku jerin shirin abubuwan da APC ta tsara yi kamar haka:

 1. Zuwan yardaddun Wakilan Jam'iyya na Kasa - karfe 10 na safe zuwa 1 na rana
 2. Isowar mambobin kwamitin tsare-tsare na kasa (CECPC) - karfe 1:30 na rana
 3. Zuwan gwamnonin jihohin jam'iyyar APC, 'yan majalisun tarayya, ministoci da shugabannin jam’iyya - karfe 1:30 na rana zuwa -2:00 na rana
 4. Zuwan shugaban majalisar wakilai - karfe 2:10 na rana
 5. Zuwan shugaban majalisar dattawa - karfe 2:20 na rana
 6. Zuwan shugaban kwamitin riko na kasa (CECPC) - karfe 2:30 na rana
 7. Zuwan Mataimakin Shugaban Kasa - 2:45 na rana
 8. Zuwan Shugaban Kasa - Karfe 3:15 na yamma
 9. Taken Kasa - 3:30 na yamma
 10. Bude taro da addu'a - 3:35 na yamma
 11. Sakon fatan alheri daga bangaren matasa, bangaren mata, bangaren nakasassu (PLwD) da bangaren mazauna kasashen waje - 3:40 zuwa 4:50 na yamma
 12. Jawabin Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC da Wakilan Gwamnoni daga kowace shiyya ta siyasa guda shida - 4:50 zuwa 5:20 na yamma
 13. Hutun rabin lokaci - 5:20 zuwa 5:25 na yamma
 14. Jawabin shugaban majalisar wakilai - 5:25 zuwa 5:30 na yamma
 15. Jawabin Shugaban Majalisar Dattawa - 5:30 zuwa 5:35 na yamma
 16. Jawabin mataimakin shugaban kasa - 5:35 zuwa 5:40 na yamma
 17. Jawabin na musamman daga Shugaban Kasa - 5:40 zuwa 5:55 na yamma
 18. Jawabin Maraba daga Shugaban Kwamitin Tsare-tsare na Kasa da gabatar da kudurori - 5:55 zuwa 6:10 na yamma

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Jiga-jigan sanatocin APC za su gana da shugaba Buhari a yau Alhamis

i. Kudin amincewa da gyaran kundin tsarin mulki

ii. Kudurin amincewa da duk ayyukan da CECPC ke gudanarwa

19. Jawabin Shugaban Kwamitin Zabe - 6:10 zuwa 6:20 na yamma

20. Zabe a ofisoshin shiyya da na kasa na jam'iyyar APC

21. Hutun na dan lokaci

22. Kidaya da Tattara Kuri'u

23. Bayyana Sakamako / Rantsar da sabbin zababbu a jam'iyya

24. Jawabin karba daga sabbon zababben shugaban jam'iyyar APC na kasa

25. Kudirin rufe babban taron kasa na 2022

26. Jawabin Rufewa daga Sakataren jam'iyya na Kasa

27. Rufewa da addu'a

28. Taken Kasa

29. Tashi daga taro

Akwai matsala: PDP ta gargadi INEC kan sanya ido da halartar taron gangamin APC

A wani labarin, PDP ta gargadi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da kada ta halarci taron gangamin jam’iyya mai mulki APC ko sanya ido kan lamurranta yayin tdaron.

Legit.ng ta tattaro cewa jam’iyyar PDP ta yi wannan gargadin ne a wata sanarwa da kakakinta Debo Ologunagba ya fitar a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Kada mu kuskura mu bari PDP ta taba karagar mulki da kazantar hannunta, Buhari

Jam'iyyar adawar ta bayyana taron na ranar Asabar 26 ga watan Maris a matsayin taron hauragiya da jam'iyyar mai mulki ta shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel