Kwastam Ta Kama Motar Dangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

Kwastam Ta Kama Motar Dangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

  • Hukumar kwastam a Najeriya ta yi nasarar cafke wata motar Dangote makare da shinkafar waje
  • Hukumar ta bayyana kame motar dauke da buhuna 250 na haramtacciyar shinkafar ta kasar waje
  • Hakazalika a wani yankin hukumar ta kame wasu haramtattun kayayakin da suka hada da fatan jaki, ganyen wiwi da sauransu

Legas - Kwantrolla Janar na Kwastam, Team A Unit, Mohammed Yusuf, ya ce jami'an hukumar sun kwace wata motar babban Dangote makare da buhun shinkafa na kasar waje 250 da aka haramta shigo da su.

Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Ikeja, Legas, yayin taron manema labarai inda ya bada jawabin ayyukan da suka yi cikin makonni hudu a sassa daban-daban, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Anambra: Laifuka 3 da suka jawo aka kama tsohon gwamna Obinao garin tserewa Amurka

Kwastam Ta Kama Motar Kamfanin Dangote Da Buhun Haramtattun Shinkafa 250
Kwastam Ta Kama Motar Kamfanin Dangote Da Buhun Haramtattun Shinkafa 250. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa a cikin kayan da aka kwace akwai kwantena ta katako mai tsawon kafa 20; buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 1000; taya na gwanjo guda 3,143; kunshin tufafin gwanjo 320; Buhun fatar jaki 44 da ganyen wiwi kilogiram 137.3.

"Ina farin cikin bayyana cewa cikin makonni hudu, tawaga ta Strike Force Team A, ta karbi N648,300,986 a matsayin haraji. Ta kuma kwace kaya da kudin harajinsu ya kai N373,629,700.
"Ina son in jadada cewa ba mu daukan aiki da wasa musamman aiki mai muhimmanci irin wannan. Masu fasakwabri da ke tunanin za su yi amfani da wannan damar su yi mummunan aikinsu za su sha mamaki," in ji shi.

Kakakin Kwastam, Peter Duniya, ya tabbatar da kama motar kamfanin Dangoten

Kara karanta wannan

Kamfanonin sadarwa su na maganar kara farashin yin wayar salula saboda tsadar mai

Mai magana da yawun sashin, Peter Duniya, ya tabbatar da cewa an kama motar kamfanin Dangote dauke da haramtatun kayan.

"Motar kamfanin Dangote na daya daga cikin kayayyakin da muka kama," ya kara.

Kwastam ta kama litar man fetur 30,150 daga hannun masu fasakwabri zuwa kasar waje

A wani labarin mai kama da wannan, Jami'an hukumar Kwastam, na yankin Seme, a wani samamen cikin dare sun kama litar man fetur 30,150 da ake karkatar zuwa Jamhuriyar Benin, Daily Trust ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne kusan makonni biyu bayan hukumar ta yi wani kame mai kala da wannan.

Kwantrollan yankin Seme, Bello Mohammed Jibo, ya ce an yi kamen na baya-bayan nan ne a ranar 12 ga watan Janairun 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel