Kotu Ta Yi Fatali Da Ƙudirin Rufe Wani Masallaci a Kasar Faransa

Kotu Ta Yi Fatali Da Ƙudirin Rufe Wani Masallaci a Kasar Faransa

  • Wata kotun kasar faransa ta soki kudirin gwamnatin kasar Faransa na rufe wani masallaci da ke kusa da garin Bordeaux
  • Lauyan kungiyar masallacin Al Farouk, Sefen Guez Guez a ranar Laraba ya ce kotun ta ce rufe masallacin rashin adalci ne
  • Dama majalisar tarayyar kasar a watan Yulin da ya gabata gabatar da wannan kudirin duk da yadda wasu ‘yan majalisa da jama’a suka nuna rashin yardarsu

Kasar Faransa - Wata kotun kasar Faransa ta rushe kudirin gwamnatin kasar na rufe wani masallaci da ke garin Bordeaux, Daily Trust ta ruwaito.

Sefen Guez Guez, lauyan kungiyar masallacin Al Farouk, a ranar Laraba ya ce kotun Bordeaux Administrative ta rushe kudirin gwamnatin na ranar 14 ga watan Maris na rufe masallacin har tsawon watanni 6.

Kara karanta wannan

Ramadan: Saudi ta ji uwar bari bayan ta nemi ta dakatar da haska sallolin dare da azumi

Kotu Ta Yi Fatali Da Kudirin Rufe Wani Masallaci a Kasar Faransa
Kotu Ta Yi Watsi Da Kudirin Rufe Wani Masallaci a Kasar Faransa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kula da yadda kotun ta yanke hukuncin inda ta ce babu adalci a batun rufe masallacin. Ta kara da cewa masallacin yana zama wurin haduwar musulmai.

An rufe masallacin Al Farouk da ke yankin Pessac kusa da garin Bordeaux bisa zargin shi da kare musuluncin tsageranci da kuma yada akidar salafanci.

Ko bayan gwamnatin ta kafa dokar, musulmai da masu rajin kare hakkin bil’adama sun dinga sukarta

Daily Trust ta ruwaito yadda a watan Augusta, hukuma mafi karfi ta kundin tsarin mulkin Faransa ta amince da wata doka wacce aka dinga caccaka ta ware musulmai.

An mika dokar ga majalisar tarayyar kasar a watan Yuli duk da yadda masu rajin kare hakkin bil adama da wasu ‘yan majalisa suka dinga suka.

An dinga sukar dokar akan kai hari ga al’ummar musulman yankin, wadanda su ne suka fi yawa a Europe, inda suke da mabiya miliyan 3.35, sannan an kafa dokar hana walwala na harkokin rayuwarsu na yau da kullum.

Kara karanta wannan

Maraba da Ramadan: Gwamnatin Ganduje ta yi gyara a Kalandar makarantun Kano saboda zuwan Azumi

Dokar ta bai wa jami’ai damar shiga harkokin kungiyoyin su da masallatai tare da lura sa harkokin kudaden kungiyoyin musulmai da kungiyoyi masu zaman kansu.

Gwamnatin Faransa ta dade tana rufe masallatai

Har ila yau, dokar ta takaita wa musulmai damar zabar darussan makarantu har sai ta amince. Sannan karkashin dokar, an haramta wa marasa lafiya damar zabar jinsin likitan da zai duba su ko kuma addini.

Kungiyoyi masu zaman kansu sun dade suna caccakar Faransa, musamman majalisar dinkin duniya, akan yadda take harin musulmai tare da cutar da su da dokokinta.

Tun watan Fabrairun 2018, Faransa ta dade tana iko da masallatai 25,000, makarantu, kungiyoyi da masana’antu. Kuma ta rufe guda 718, ciki har da masallatai 20, kamar yadda aka wallafa a wani rahoton 2 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel