Kada ka yaudari Tinubu, idan ba haka ba karshenka ba zatayi kyau ba: Fasto ga Osinbajo

Kada ka yaudari Tinubu, idan ba haka ba karshenka ba zatayi kyau ba: Fasto ga Osinbajo

  • Wani babban fasto a jihar Neja ya yi kira ga Farfesa Yemi Osinbajo kada ya sake yace zai yi takara
  • Akalla mutum goma sun bayyana niyyar takara a zaben kujerar shugaban kasa a zaben 2023
  • Osinbajo wanda yanzu mataimakin shugaban kasa ne zai iya neman takarar kujerar shugaban kasa

Neja - Fasto Isaac Moses na cocin Amazing Revelation Divine Ministry, Suleja, jihar Niger, ya gargadi mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, kada ya yaudari Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Faston ya bayyana cewa idan Osinbajo ya yaudari Tinubu, hakan na iya zama karshen siyasarsa.

Ya shawarci Osinbajo cewa yaudara zunubi ne kuma a matsayinsa na Fasto ya san da haka, rahoton DailyPost.

Yana koro aya daga littafin Bible, ya gargadi Osinbajo cewa kada "ka yaudari wani."

A cewarsa:

"Idan kayi, zaka ji kunya wajen mutane, kuma mutuncinka ya zube."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kamar yadda aka min wahayi, akwai karshe mara kyau idan Osinbajo ya nemi takara. Abun ba zai yi kyau ba."
"Osinbajo namu ne. Kiristoci na son sa kuma suna ganin girmansa. Amma abubuwan dake faruwa kwanan nan da ban damuwa."

Fasto ga Osinbajo
Kada ka yaudari Tinubu, idan ba haka karshenka ba zatayi kyau ba: Fasto ga Osinbajo Hoto: Laolu Akande
Asali: Facebook

Me yasa har yanzu ya ki magana kan lamarin takara?

Faston ya cigaba da cewa shin wani dalili ya hanashi fitowa fili ya fadi cewa bai da niyyar takara don kashe wutan jita-jitan dake yawo.

Yace:

"Misali, ya ki fitowa karyata labaran niyyar takara. Wannan ba halin Kirista bane. Ya kamata ace yayi bayani."
"Duk da Tinubu Musulmi ne, shine babban wanda ya tsayawa Osinbajo tsawon shekaru."
"Lokacin Osinbajo zai zo."

Mu muka kashe Najeriya, dole tare mu zamu gyara: Bola Tinubu

Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa dukkanmu muka kashe Najeriya kuma mu zamu iya gyarata.

Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a lakcan bikin yaye daliban jami'ar jihar Legas LASU.

Ya samu wakilcin mataimakin gwamnan jihar Legas, Dr Obafemi Hamzat.

A kan rashin aikin yin matasa, Tinubu ya ce rashin aiki da aiki babu albashin kwarai tsakanin matasa ya kai 60%, kuma wajibi ne a magance hakan.

Tinubu yace samawa matashin birane aikin yi, aikin noma, harkar gidaje, ilimi, tattalin arziki da manyan ayyuka ya kamata gwamnati ta mayar da hankali.

Tinubu ya bada kyautar cibiyar karatu na kimanin kudi biliyan daya ga makarantar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel