Najeriya ta fi bukata ta: Abokin tafiyar Atiku ya ayyana aniyarsa ta gaje Buhari a 2023

Najeriya ta fi bukata ta: Abokin tafiyar Atiku ya ayyana aniyarsa ta gaje Buhari a 2023

  • Dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP a zaben 2019 ya sake fitowa takara, amma yanzu a matsayin shugaban kasa
  • Ya bayyana cewa, Najeriya na bukatar shugaba irinsa domin ciyar da kasar gaba yadda ya kamata
  • Ya bayyana aniyarsa ne a gaban sarakunan gargajiyar Anamba, inda ya nemi albarkarsu da shawarinsu

Dan takarar mataimakin shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2019, Mista Peter Obi, ya bayyana sha’awarsa tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya a zaben 2033.

Daily Trust ta ce, Obi ya bayyana hakan ne a gaban sarakunan gargajiya a dakin taro na gwamnatin jihar Anambra, Agu- Awka a jihar Anambra.

Ya ce ya yanke shawarar fara bayyana aniyarsa a gaban sarakuna ne domin neman albarkarsu, ya ce yana bukatar addu’o’i da goyon bayansu domin ganin ya samu nasara.

Kara karanta wannan

Umahi Ya Ziyarci Buhari, Ya Ce Takararsa Na Shugabancin Ƙasa 'Aikin Allah' Ne

Peter Obi ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa
Najeriya ta fi bukata ta: Na kusa da Atiku ya ayyana aniyarsa ta gaje Buhari a 2023 | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewarsa:

“Ina magana da sarakunan gargajiya domin idan mutum ya fara wata tafiya dole ne ya fara gaya wa ubansa.
“Ina gaya muku a matsayinku na iyaye na cewa na fito ne domin in tsaya takarar shugabancin Najeriya.
“Kun san ni kuma kun san yadda Najeriya take a yau. A 2019 na fito tare da Atiku a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa amma yau ina son fitowa da kaina.
“Na zo ne domin neman albarkarku a matsayinku na sarakunan gargajiya na Jihar."

Tsohon gwamnan na Anambra ya ce zai tsaya takarar ne idan PDP ta ware tikitin shugabancin kasar zuwa yankin Kudu.

'Najeriya na bukata ta', inji Peter Obi

Obi ya ce bayan nazartar Najeriya cikin tsanaki, ya gano cewa Najeriya na cikin wani yanayi, kuma kasar na bukatar mutum irinsa da zai ciyar da ita gaba.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya ayyana kudurinsa na gaje kujerar Buhari a zaben 2023

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce ya yi imani da gaskiyar Najeriya a dunkule tsintsiya daya.

Obi ya ce yana cikin fafutukar ciyar da Najeriya gaba.

Atiku shugaba na ne, inji Obi

A ranar Laraba, Mista Obi ya halarci wani taron da Atiku ya hada don bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, kamar yadda Channels Tv ta ruwaitoo.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya halarci taron da abokin hamayyarsa ya shiya, Obi ya ce Atiku Abubakar “shugabana ne” kuma “siyasa ba yaki ba ce.”

Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa

A wani labarin, wata kungiya mai suna abokan Tambuwal sun siya wa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fom din takarar zaben shugaban kasa a jam'iyyar PDP.

Kungiyar, karkashin jagorancin Aree Akinboro, sun siya fom din ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja, The Cable ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

PDP ta tsayar da ranar 28 ga watan Mayu domin zaben yan takarar da za su wakilci jam'iyyar a zaben na 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel