Buhari ya bada izinin fitar da kudi N14bn don baiwa marasa digiri 500,000 aikin N-Power, Sadiya

Buhari ya bada izinin fitar da kudi N14bn don baiwa marasa digiri 500,000 aikin N-Power, Sadiya

  • A zaman FEC na ranar Laraba, an bada izinin horas da marasa digiri rabin miliyan cikin shirin N-power
  • Minista Sadiya Farouq ta ce za'a yi amfani da ma'aikatun gwamnati hudu wajen horas da matasan
  • Sadiya tace za'a baiwa matasan jari don fara nasu kasuwancin bayan kammala horon

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bada izinin sakin sama da N14 billion don horas da matasa marasa digiri 500,000 a shirin N-Power na tsawon watanni tara.

Hakan ya bayyana a zaman majalisar zartaswar tarayya FEC da shugaban ya jagoranta ranar Laraba, 23 ga Maris, 2022 a fadar shugaban kasa, Aso Villa.

Ministar jin kai da jin dadin jama'a, Hajiya Sadiya Farouq, ta bayyana hakan ga manema labarai bayan zaman, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun bindige Shahararren ɗan kasuwa har Lahira

Hajiya Sadiya
Buhari ya bada izinin fitar kudi N14bn don baiwa marasa digiri 500,000 aikin N-Power, Sadiya Hoto: Sadiya-farouq
Asali: Twitter

Ta yi bayanin cewa za'a yi amfani da N14 billion wajen aiki tare da hukumomin gwamnati hudu da zasu baiwa wadannan matasa horo na tsawon watanni tara.

Tace:

"Yau (ranar Laraba), ma'aikatar jinkai, manejin annoba da jin dadin al'umma ta gabatar da kudiri ga majalisa ne neman izinin aiki tare da hukumomin gwamnatin tarayya hudu wajen horas da matasan N-Power marasa digiri."
"Wadannan marasa digiri 500,000 za'a horas a ayyuka daban-daban."
"Hukumomin sun hada da makarantar fasahar sufuri ta kasa NITT, asusun lamunin horo ITF, makarantar yawon ganin ido da hutu da kuma makarantar cigabar kayayyakin ruwa."

Ta kara da cewa a karshen horon na watanni tara da za'a yi, za'a baiwa matasan jari don fara nasu kasuwancin.

N-Power Batch C: Buhari ya bada umurnin a kara diban mutum milyan 1, Minista Sadiya

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Gwamna Tambuwal ya gana da IBB da Abdulsalami, ya bayyana shirin ‘yan takarar PDP

Ministar harkokin jin kai da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq ta bayyana cewa kimanin yan Najeriya milyan shida da rabi suka nemi zango na uku na shirin aikin N-Power.

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin daukar matasa aikin wucin gadi na N-Power ne a shekarar 2016.

Shirin na baiwa matasa aikin koyarwa ko noma tsawon shekaru biyu kafin a yaye su.

Kawo yanzu, an yaye wadanda sukayi musharaka a zango na daya A da zango na biyu B.

Asali: Legit.ng

Online view pixel