N-Power Batch C: Buhari ya bada umurnin a kara diban mutum milyan 1, Minista Sadiya

N-Power Batch C: Buhari ya bada umurnin a kara diban mutum milyan 1, Minista Sadiya

  • Kimanin matasan Najeriya milyan shida da rabi suka nemi aikin N-Power zango na uku na gwamnatin tarayya
  • Ministar harkokin jin kai da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq ta bayyana haka
  • A cewarta kawo yanzu mutum 510,000 aka dauka kuma za'a dauki karin sabbin mutane 490,000

Ministar harkokin jin kai da jin dadin al'umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq ta bayyana cewa kimanin yan Najeriya milyan shida da rabi suka nemi zango na uku na shirin aikin N-Power.

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin daukar matasa aikin wucin gadi na N-Power ne a shekarar 2016.

Shirin na baiwa matasa aikin koyarwa ko noma tsawon shekaru biyu kafin a yaye su.

Kawo yanzu, an yaye wadanda sukayi musharaka a zango na daya A da zango na biyu B.

Kara karanta wannan

Dinbin mutane za su rasa aikin yi yayin da Naira ta kara durkushewa kasa a kasuwar canji

Minista Sadiya
N-Power Batch C: Buhari ya bada umurnin a kara diban mutum milyan 1, Minista Sadiya Hoto: FMHDSI
Asali: UGC

Hajiya Farouq ta bayyana adadin wadanda suka nemi na zango na uku ne a taron kaddamar da tsarin kula da yan gudun hijra a Abuja, rahoton Punch.

Farouq tace:

"Ma'aikatar ta samu nasarar yaye mutum 500,000 na zangon A da B a 2020 kuma mutum milyan 6.4 sun nemi zangon C.
"Karkashin zango na uku C dibar farko, an dauki mutum 510,000 kuma suna amfana yayinda za'a dauki karin mutum 490,000 bisa izinin shugaban kasa na a kara mutum milyan daya."

Zamu kashe tsutsar ciki na daliban Najeriya milyan daya, Hajiya Sadiya Farouq

Ma'aikatar tallafi da jin kai ta bayyana cewa zata baiwa daliban makarantun firamare guda milyan daya maganin kashe tsutsar ciki don inganta lafiyarsu.

Shugaban shirin NSIP, Dr Umar Bindir, ya bayyana hakan a zaman shirye-shirye na tsawon kwana biyar dake gudana a birnin tarayya Abuja ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Sojan Najeriya da ya sha Kwayar Maye ya bindige mutane har Lahira a Borno

Kamfanin dillancin labarai NAN yace daya daga cikin manufofin zaman shine samar da kayayyakin kashe tsutsar cikin dalibai.

Mr Bindir, wanda ya samu wakilcin mataimakiyar diraktar shirye-shirye, bincike da lissafe-lissafe a ma'aikatar, Safiya Sani, ya bayyana muhimmancin kashe tsutsar cikin don inganta lafiyansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel