Yadda wani ɗan kasuwa ya halaka yan bindigan da suka yi garkuwa da shi, ya dawo gida

Yadda wani ɗan kasuwa ya halaka yan bindigan da suka yi garkuwa da shi, ya dawo gida

  • Wani ɗan kasuwa a Ondo ya yi jarumta a sansanin yan bindiga ya kashe mutum biyu yayin da bacci ya ɗauke su
  • Bayanai sun nuna cewa mutumin ya yi kamar yana bacci mai nauyi, suma suka kwanta sai ya tashi ya ɗauki makamansu
  • Hukumar yan sandan jihar Ondo, ta tabbatar da aukuwar lamarin, amma tace ba gaskiya bane maganar kashe yan garkuwan

Ondo - Wani ɗan kasuwa mai siyar da Koko a yankin Supare Akoko, Mai suna, Idowu Shaba, ya samu nasarar kashe mutanen da suka yi garkuwa da shi bayan bacci ya sace su a sansani.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa, Shaba, ya samu kubuta ne daga hannun yan bindigan bayan sun tsunduma bacci.

Bayanai sun nuna cewa yan bindiga sun yi garkuwa da shi ne a kan hanyar Idoani domin halartar taron Coci tare da wasu mutane a wani jeji dake tsakanin kauyukan Afo da Idoani.

Kara karanta wannan

Shugabancin APC: Jerin Sunayen yan takarar da suka yi fatali da umarnin Buhari, suka mika Fam Hedkwata

Yan bindiga
Yadda wani ɗan kasuwa ya halaka yan bindigan da suka yi garkuwa da shi, ya dawo gida Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Maharan sun tasa ƙeyarsa da wata budurwa zuwa sansaninsu a cikin ƙungurmin dajin kuma suka ɗaure musu hannuwa.

Hakanan kuma sun tuntuɓi iyalansu, sun nemi a haɗa musu naira Miliyan N10m kuɗin fansa kafin su sako su.

Yadda ɗan kasuwan ya kubuta?

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa:

"Shaba ya yi kamar yana bacci mai ɗankaren nauyi kuma ya yi sa'a hakan ya sa masu gadinsa suka fara bacci. Bai yi wata-wata ba ya yi amfani da damarsa ya ɗauke makamansu."
"Sannan ya yi amfani da wata wuƙarsu mai kaifii ya kashe biyu daga cikin su, ya jikkata ɗayan wanda ya samu nasarar tserewa.
"Ya ɗauki bindigar yan ta'addan AK-47 da wukake, kuma ya kubutar da ɗaya yarinyar. Bindigar na ɗauke da bayanan yan sanda."

Kara karanta wannan

Dubun wani ƙasurgumin shugaban yan bindiga da ya addabi hanyar Kaduna-Abuja ya cika

Hukumar yan sanda ta samu labari?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ondo, DSP Fumilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta musanta rahoton dake cewa Shaba ya kashe masu garkuwa.

Ta yi bayanin cewa mutumin ya faɗa wa yan sanda cewa ya samu nasarar tsero wa daga sansanin masu garkuwa ne bayan bacci ya kwashe su.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari Kaduna, sun aikata babbar ɓarna kan mutane

Yan ta'adda sun kai hari ƙauyen Agunu Dutse dake ƙaramar hukumar Ka

chia a jihar Kaduna da tsakar daren Alhamis.

Bayanai daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun jikkata wani da harbi, sun kuma yi awon gaba da mutum 47.

Asali: Legit.ng

Online view pixel