Innalillahi: Wata gobara ta sake barkewa, ta yi kaca-kaca da gidaje a jihar Legas

Innalillahi: Wata gobara ta sake barkewa, ta yi kaca-kaca da gidaje a jihar Legas

  • Wata mummunar gobara ta tashi a jihar Legas, inda ta lalata dukiyoyi a wani yankin Marine Beach na Apapa
  • Wannan lamari dai ya jawo konewar wasu gidajen katako da ke yankin, inda har yanzu ake ci gaba da kashe ta
  • Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa a jihar Legas ta ba da labarin yadda ake ci gaba da shawo kan gobarar

Legas - Sa’o’i kadan bayan wata gobara da ta tashi ta lalata kayyakin miliyoyin Naira a kasuwar Apongbo da ke tsibirin Legas, an sake samun barkewar wata gobarar a yankin Marine Beach da ke Apapa a jihar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, gobarar ta biyu ta lalata wasu kananan gidajen kwana a yankin.

Gobara ta yi kaca-kaca da gidaje a jihar Legas
Innalillahi: Wata gobara ta sake barkewa, ta ci duniyoyi da yawa a jihar Legas | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 12:45 na rana, kamar yadda wasu masu aikin ceto a yankin suka bayyana.

Kara karanta wannan

Dinbin mutane za su rasa aikin yi yayin da Naira ta kara durkushewa kasa a kasuwar canji

Yawancin gine-ginen da abin ya shafa dai gidaje ne na katako inda ake sayar da man ababen hawa a cikin jarkoki.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) Ibrahim Farinloye, ya ce gobarar ta tashi ne daga wasu gidajen da ke yankin.

Ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 12:45 na rana kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto tana ci gaba da barna.

A cewarsa:

"Amma an shawo kan lamarin yayin da jami'an kashe gobara ke fafatawa da kashe gobarar."

Kafin wannan gobara, rahotanni sun bayyana cewa, wata gobara ta kama a gadar Eko, inda ta tafka barna mai yawa.

Jim kadan bayan faruwar hakan ne jaridar Guardian ta ce, gwamnatin Legas ta ba da umarnin rufa dukkan zirga-zirga a yankin gadar saboda gujewa barna.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Bayan watsi da kujerar da Ganduje ya bashi, Yakasai ya fita daga APC

Gobara ta tashi Babban Asibitin Asokoro a Abuja

A wani labarin, wani sashi na babban asibitin yankin Asokoro da ke birnin tarayya Abuja ya kama da wuta, rahoton The Punch.

Ba bu tabbas ko an rasa rai sakamakon gobarar. Channels Television ta rahoto cewa daga bisani an yi nasarar kashe wutan.

Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, cikin wani sako da ta wallafa a Twitter ta ce: "Jami'an mu sun yi nasarar kashe gobarar da ta tashi a Babban Asibitin Asokoro a Abuja."

Asali: Legit.ng

Online view pixel