'Karin bayani: Gobara ta tashi Babban Asibitin Asokoro a Abuja

'Karin bayani: Gobara ta tashi Babban Asibitin Asokoro a Abuja

FCT, Abuja - Wani sashi na babban asibitin yankin Asokoro da ke birnin tarayya Abuja ya kama da wuta, rahoton The Punch.

Yanzu-Yanzu: Gobara ta tashi a asibitin Asokoro a Abuja
Gobara ta tashi a asibitin Asokoro a Abuja. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Ba bu tabbas ko an rasa rai sakamakon gobarar.

Channels Television ta rahoto cewa daga bisani an yi nasarar kashe wutan.

Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, cikin wani sako da ta wallafa a Twitter ta ce:

"Jami'an mu sun yi nasarar kashe gobarar da ta tashi a Babban Asibitin Asokoro a Abuja."

Ku dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel