Kwamitin bincike ya aike wa Abba Kyari sammaci, an sanar masa ranar gurfana

Kwamitin bincike ya aike wa Abba Kyari sammaci, an sanar masa ranar gurfana

Kwamitin bincike mai zaman kansa ya sanya ranar 30 ga Maris ga dakataccen DCP Abba Kyari a kan gurfana a gaban kotu kan zargin kama wasu mutane uku da yayi ba bisa kaida ba kuma suka shigar da kara.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kwamitin yana binciken zargin take hakkin dan Adam da rusasshiyar rundunar yaki da fashi da makami (SARS) da wasu sassan ‘yan sandan Najeriya ke yi.

Kwamitin bincike ya aike wa Abba Kyari sammaci, an sanar masa ranar gurfana
Kwamitin bincike ya aike wa Abba Kyari sammaci, an sanar masa ranar gurfana. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Masu shigar da kara, Ambrose Mairungu, da Blessing Dung, a cikin wata kara mai lamba 2020/IIP-SARS/ABJ/205 sun yi zargin cewa Yakubu Danjuma, Ibrahim Daniel da Choji, mijin Dung an kama su ba bisa ka’ida ba tare da tsare su, azabtarwa da kuma cin mutuncin duk kuma Kyari ne yayi hakan.

Kara karanta wannan

Kotu ta sake ba Sowore gaskiya, ta ci DSS tara saboda cafke ‘Dan gwagwarmaya tun 2019

A ranar 11 ga watan Maris kwamitin binciken ya umurci shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA mai ritaya, Brig.-Gen. Buba Marwa zai fito da Kyari a ranar 22 ga Maris, don kare kansa.

Sai dai a martanin da aka bayar ga wannan umarni, Abdullahi Haruna, SAN, lauyan Kyari ya rubuta wasikar gudanarwa ga shugaban kwamitin.

Yana neman a gabatar da duk koke-koke da aka ambaci sunan Kyari don ba shi damar yin nazari da kuma amsa su yadda ya kamata, Daily Trust ta ruwaito.

Don haka ya roki kwamitin da ya ba shi damar gudanar da shari’ar irin wannan, sannan ya yi addu’ar a ba shi watanni biyu.

Garba Tetengi, SAN, wanda ya wakilci shugaban, Mai shari’a Suleiman Galadima mai ritaya, ya ce kwamitin ba shi da lokaci amma zai iya ba shi mako guda.

Kara karanta wannan

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

Daga nan ya dage ci gaba da sauraren karar PW1 da 2 har zuwa ranar 30 ga Maris.

A cikin karar, Dung, matar wanda aka azabtar ta uku ta shaida wa kwamitin cewa a ranar 17 ga Disamba, 2019, mijin ta ya samu kiran waya daga abokinsa, Danjuma don ganawa a wajen gidan.

“Na bi mijina har waje, sai na hango wasu motoci guda biyu masu duhun gilashi da aka rubuta IRT a kansu.
"Na ga 'yan sanda dauke da makamai da suka fito daga cikin motoci, a take suka daure mijina, suka yi harbi a iska suka tafi da shi," a cewar ta.

Ta kuma roki kwamitin da ya basu diyyar Naira miliyan 10.

Abba Kyari ya sake shiga 3, kwamitin binciken EndSARS na bukatar NDLEA ta mika shi

A wani labari na daban, a kwamitin dake bincikar zargin take hakkin bil'adama da tsohuwar hukumar SARS ta 'yan sandan Najeriya ke yi, ta yi kira ga Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi da ta mika dakataccen DCP Abba Kyari gaban ta.

Kara karanta wannan

Kwastam Ta Kama Motar Ɗangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

Kwamitin mai zaman kanta ta bukaci shugaban NDLEA, Buba Marwa, da ya mika ma ta Kyari a ranar Talata, 22 ga watan Maris.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda, Shugaban kwamitin, Alkali mai ritaya Suleiman Galadima, wanda John Martin ya gabatar, ya umarci kwamandan na IGP-IRT, Tunde Disu, da ya tabbatar an gabatar da Kyari a wannan ranar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel