Abba Kyari ya sake shiga 3, kwamitin binciken EndSARS na bukatar NDLEA ta mika shi

Abba Kyari ya sake shiga 3, kwamitin binciken EndSARS na bukatar NDLEA ta mika shi

  • Kwamitin binciken cin zarafi da take hakkin dan Adam da 'yan ssanda SARS ke yi na bukatar a mika mata Abba Kyari
  • Kwamitin karkashin shugabancin Sulaiman Galadima, alkali mai ritaya, ya bukaci Buba Galadima da ya mika musu dan sanda
  • Hakan ya biyo bukatar da aka mika gaban shugaban IGP-IRT, Tunde Dirsu, da ya miko dan sandan amma yace baya karkashin ikon 'yan sanda yanzu

A kwamitin dake bincikar zargin take hakkin bil'adama da tsohuwar hukumar SARS ta 'yan sandan Najeriya ke yi, ta yi kira ga Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi da ta mika dakataccen DCP Abba Kyari gaban ta.

Kwamitin mai zaman kanta ta bukaci shugaban NDLEA, Buba Marwa, da ya mika ma ta Kyari a ranar Talata, 22 ga watan Maris.

Abba Kyari ya sake shiga 3, kwamitin binciken EndSARS na bukatar NDLEA ta mika shi
Abba Kyari ya sake shiga 3, kwamitin binciken EndSARS na bukatar NDLEA ta mika shi. Hoto daga Abba Kyari
Asali: Facebook

Daily Nigerian ta ruwaito yadda, Shugaban kwamitin, Alkali mai ritaya Suleiman Galadima, wanda John Martin ya gabatar, ya umarci kwamandan na IGP-IRT, Tunde Disu, da ya tabbatar an gabatar da Kyari a wannan ranar.

Kara karanta wannan

Kaduna: Baya ga hari a masallaci, 'yan bindiga sun hallaka mutane, sun sace wasu mata

Kamar yadda Martin ya ce, ana bukatar ganin zakakurin dan sandan, duba da yadda mai korafin ya ambaci sunan Kyarin a farkon zaman da aka yi.

"Shaidar ya tabbatar da cewa, Kyari yayi alkawarin tuntubar shi a kan rashin samar da mutanen, amma har yanzu ba amo babu labarin su.
"Wannan umarnin an badashi ne, domin mutane ukun da IGP -IRT ta kamar. A halin yanzu, babu wanda ya san inda Yakubu Danjuma, Ibrahim Daniel da Choji Dung suke."

Bukatar gabatar da Kyarin ta zo ne bayan lauyan kwamitin, Halilu Adamu, ya sanar da cewa Kyari na hannun NDLEA.

Haka zalika, lauyan rundunar, James Idachaba, ya bayyana wa kwamitin yadda NPF ba za ta iya gabatar da Kyari ba, tunda yanzu baya hannun 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a Kaduna, rayuka sun salwanta

Da farko, kwamitin ta umarci ofishin sifeta janar na 'yan sanda da ya gabatar ma ta da sunayen wadanda ake zargin guda uku.

Kafin wannan bukatar, babban kotun shari'a ta Abuja ta umarci sakin mutanen da aka ambata, amma har zuwa yanzu ba a

yi hakan ba.

Zargin safara: Yadda Abba Kyari ya yi aiki da kungiyar dillalan kwayoyi a Brazil, NDLEA

A wani labari na daban, hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta ce, babu ruwan ma'aikatan ta da sabgar hodar iblis mai nauyin kilogram 25 da ya hada da tawagar yan sanda karkashin jagoranci mataimakin kwamishinan 'yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari.

A wata takarda da kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a ranar Laraba, ya dora laifin a kan ma'aikatan hukumar 'yan sanda da kuma yadda wadanda ake zargin suka shirin shigo da haramtattun ababen daga Addis Ababa, Ethiopia.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Gwarazan yan sanda sun kama yan bindiga 200, yan fashi 20 a jihar Kaduna

'Yan sanda ne ke ikirari a wata takarda da suka fita ranar Litinin cewa, ma'aikatan NDLEA suna da sa hannu a harkallar. Sai dai, ba tare da nuna martani ga maganar 'yan sandan ba Mr Babafemi ya nuna rashin amincewa da ikirarin, wanda ya siffanta da tuntuben harshe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel