Ziyarar Legas: Buhari ya dura masana'antar taki mafi girma a Afrika, mallakin Dangote

Ziyarar Legas: Buhari ya dura masana'antar taki mafi girma a Afrika, mallakin Dangote

  • A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dura masana'antar samar da takin zamani ta Dangote
  • Shugaban ya kai ziyara birnin Legas ne domin bude wasu ayyuka a jihar ta Legas tare da rangadi a wasu sassa
  • Rahotanni sun bayyana cewa, masana'antar ta Dangote itace mafi girma a nahiyar Afrika idan aka yi la'akari da girmanta

Legas - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Ibeju Lekki da ke jihar Legas domin halartar bikin bude katafaren kamfani mai darajar biliyoyin daloli na takin zamani mallakin Dangote.

Kamfanin, wanda aka gina kan kudi dala biliyan 2.5, yana da karfin samar da metric tonnes miliyan uku (mt) na nau'in takin urea a duk shekara, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsaro ya tabarbare a Imo, Buhari ya ce a tura karin jami'ai da makamai

Takin Dangote
Ziyarar Legas: Buhari ya dura masana'antar taki mafi girma a Afrika, mallakin Dangote | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar dangote.com, masarrafar ita ce mafi girma wajen samar da takin Granulated Urea a nahiyar Afirka kuma ta mamaye hekta 500 na fili a yankin na Lekki.

Ana kuma sa ran masana'antar za ta kara sama da dala miliyan 400 na kudaden waje ga tattalin arzikin Najeriya ta hanyar fitar da kayayyakin taki zuwa wasu kasashen Afirka.

Haka kuma ana sa ran za ta kara karfin samar da takI kamar dai sauran kamfanoni irinsu Indorama Chemicals, dake jihar Rivers, wadanda ke samar da takin urea, ammonia da sauran nau'ika.

Shugaban zai kuma yi amfani da damar ziyarar da ya kai Legas domin rangadi a tashar jiragen ruwa ta Lekki da matatar man Dangote duk dai a jihar.

Gidan talabijin na Channels ya yada wani bidiyon lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa masana'antar.

Kara karanta wannan

Ku tara min kudi na gaji Buhari: Dan takara na neman tallafin 'yan soshiyal midiya

Ziyara: Shugaba Buhari zai dira jihar Legas, zai kaddamar da ayyuka, zai duba wasu

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Legas, inda zai duba tare da kaddamar da wasu ayyuka da ake yi a jihar.

A wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya fitar ta shafukansa na Facebook da Twitter, ya yada hotunan ayyukan da shugaban zai duba tare da kaddamarwa.

Sanarwar ta ce, shugaban zai kai ziyarar ta aiki ne a gobe Talata 22 ga watan Maris.

Wani yankin sanarwar ya bayyana cewa Buhari zai duba ayyukan da ake yi a wata tashar jirgin ruwa da ake yi a jihar ta Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel