TV mai fuka-fukai da hotunan kayan alatun da ke sabon katafaren gidan mawaki Davido

TV mai fuka-fukai da hotunan kayan alatun da ke sabon katafaren gidan mawaki Davido

  • A cikin kwanakin nan, fitaccen mawaki Davido ya bayyanawa masoyansa wasu sassan katafaren gidansa da ke Banana Island
  • Mawakin ya je wurin saka labaransa na Instagram inda ya nuna dankara-dankaran motocinsa da kuma wani irin TV mai fuka-fukai
  • A ta wajen farfajiyar katafaren gidan kuwa, an samu wurin wanka da ninkaya, kyawawan bishiyoyi da kuma wurin zama mai kyau

Kusan watanni biyu da suka gabata, fitaccen hazikin mawakin Najeriya, Davido, ya siya wa kansa sabon gida a Banana Island da ke Legas kuma yayi liyafa saboda hakan.

A wallafar kwanan nan, mawakin ya bayyana wasu sassan ciki da wajen katafaren gidan nashi.

TV mai fuka-fukai da hotunan kayan alatun da ke sabon katafaren gidan mawaki Davido
TV mai fuka-fukai da hotunan kayan alatun da ke sabon katafaren gidan mawaki Davido. Hoto daga @davido
Asali: Instagram

Aljannar duniya

Daga cikin katafaren gidan mawaki Davido, an kawatar da shi da haske masu kyau, kujeru, zane, kayan kawa da kuma wasu daga cikin lambobin yabon da ya taba karba.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Bayan watsi da kujerar da Ganduje ya bashi, Yakasai ya fita daga APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

TV mai fuka-fukai da hotunan kayan alatun da ke sabon katafaren gidan mawaki Davido
TV mai fuka-fukai da hotunan kayan alatun da ke sabon katafaren gidan mawaki Davido. Hoto daga @davido
Asali: Instagram

Duk da tsabar dukiyar da aka narka a katafaren gidan, mawakin ya yi kokarin ganin ba a cika komai ba tun daga kan fenti har zuwa zane-zane.

Kyakyawan hoton dakin hutun Davido abun kallo ne da wani dankareren TV da jamaa da yawa basu taba gani ba.

A maimakon a ajiye TV kamar yadda aka saba gani, TV sama yake yi da kasa yayin da yake bude kansa kamar fuka-fukai.

A farfajiyar gidan kuwa, bishiyoyi ne masu kyau, furanni, wurin wanka da wurin zama tare da dankararren maadanar tsadaddun motocin da ya siya kwanakin nan.

TV mai fuka-fukai da hotunan kayan alatun da ke sabon katafaren gidan mawaki Davido
TV mai fuka-fukai da hotunan kayan alatun da ke sabon katafaren gidan mawaki Davido. Hoto daga @davido
Asali: Instagram

Ka ba coci kason ta daga kudin da abokai suka hada maka, ko ka shiga wuta, Fasto ga Davido

A wani labari na daban, wani fitaccen fasto mai suna Goodheart Val Aloysius, mazaunin garin Calabar, ya yi kira ga fitaccen mawakin Najeriya, Davido, da ya zabtaro wa coci kason ta.

Kara karanta wannan

Kwastam Ta Kama Motar Ɗangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

Faston ya ce matukar mawaki Davido ya na son shiga aljanna, toh fa tabbas dole ne ya kwaso daga cikin kudaden da abokansa suka hada masa, ya bai wa coci kason ta.

Faston ya yi wannan wallafar ne a ranar ashirin ga watan Nuwamba bayan batun makuden kudin da Davido ya samu daga abokansa ya karade kafar sada zumuntar zamani.

Kamar yadda wallafar ta ce a Facebook, "Dan uwa Davido, idan har ba ka ciro kason coci daga kudin da abokai suka tara maka ba, ina tsoron ba za ka shiga aljanna ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel