Ka ba coci kason ta daga kudin da abokai suka hada maka, ko ka shiga wuta, Fasto ga Davido

Ka ba coci kason ta daga kudin da abokai suka hada maka, ko ka shiga wuta, Fasto ga Davido

  • Wani fasto mai suna Goodheart Val Aloysius, ya bukaci mawaki Davido da ya wafto wa coci kason ta daga cikin kudin da abokai suka hada masa
  • A cewar faston mazaunin garin Calabar, ya na tsoron Davido ba zai shiga aljanna ba matukar bai fitar da kason coci daga wadannan makuden kudin ba
  • A makon da ya gabata ne abokai suka tara wa mawaki Davido kudi sama da miliyan dari biyu matsayin kyautar ranar zagayowar haihuwarsa
  • Sai dai a wata bajinta da abun yabo da mawakin yayi, ya kara miliyan hamsin a kai tare da sadaukar da su ga gidajen marayun fadin kasar nan

Wani fitaccen fasto mai suna Goodheart Val Aloysius, mazaunin garin Calabar, ya yi kira ga fitaccen mawakin Najeriya, Davido, da ya zabtaro wa coci kason ta.

Kara karanta wannan

Ruwan kudi: Bidiyon yadda wasu mutane suke ta kwasar kudade a kan titi a Amurka

Faston ya ce matukar mawaki Davido ya na son shiga aljanna, toh fa tabbas dole ne ya kwaso daga cikin kudaden da abokansa suka hada masa, ya bai wa coci kason ta.

Ka ba coci kason ta daga kudin da abokai suka hada maka, ko ka shiga wuta, Fasto ga Davido
Ka ba coci kason ta daga kudin da abokai suka hada maka, ko ka shiga wuta, Fasto ga Davido. Hoto daga Goodheart Val Aloysius
Asali: Facebook

Faston ya yi wannan wallafar ne a ranar ashirin ga watan Nuwamba bayan batun makuden kudin da Davido ya samu daga abokansa ya karade kafar sada zumuntar zamani.

Kamar yadda wallafar ta ce a Facebook, "Dan uwa Davido, idan har ba ka ciro kason coci daga kudin da abokai suka tara maka ba, ina tsoron ba za ka shiga aljanna ba."

Mawakin ya wallafa lambar asusunsa na banki inda ya bukaci duk wani wanda ya san ya amfana da shi da ya bashi kyautar miliyan daya na murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Atiku ya tura wa Davido sako bayan mika kudin da aka tara masa ga marayu

Kamar yadda Davido ya wallafa, ya ce ya na son karbar Rolls Royce din sa daga tashar jirgin ruwa.

Babu shakka kafafen sada zumunta sun gigice da ganin irin ruwan naira da abokan mawakin suka dinga zuba masa.

Hatta bankin da ya ajiye lambar asusun da aka dinga masa ruwan kudi, sai da suka bukaci ganin mawakin. Sai dai a rashin samun ganinsa, sun garzaya har Dubai inda yake a lokacin domin ganawa da shi.

Sai dai wani lamarin da ya bai wa jama'a mamaki da sha'awa shi ne yadda mawakin ya sanar da cewa ya hada miliyan dari biyu kuma zai kara da kudinsa har miliyan hamsin domin rabawa gidajen marayun da ke fadin kasar nan.

Mawakin ya nada kwamitin rabon na mutum biyar wanda ya kunshi farfesoshi 3 a ciki domin su rarraba kudin.

Kudi na magana: Masoya sun tarawa Davido sama da Naira miliyan 120 a ‘yan awanni

Kara karanta wannan

Patience Jonathan ta rerawa mijinta waka mai ban dariya yayin da ya cika shekaru 64

A wani labari na daban, shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya samu miliyoyin kudi daga jama’a bayan da ya nemi a tara masa kudi.

A lokacin da Legit.ng Hausa ta ke tattara wannan rahoto a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba, 2021, sama da Naira miliyan 120 ne suka shiga asusun Davido.

Hakan na zuwa ne bayan mawakin ya yi magana a shafinsa na Instagram, inda yake tsokanar masoyansa da cewa su taimakawa sana’arsa da Naira miliyan daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel