Karin bayani: Gwamna El-Rufai ya sanya dokar hana fita a Jema'a da Kaura a jiharsa

Karin bayani: Gwamna El-Rufai ya sanya dokar hana fita a Jema'a da Kaura a jiharsa

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita a wasu kananan hukumomin jihar guda biyu
  • Wannan na zuwa ne yayin da lamurran tsaro ke kara zama barazana a yankunan da gwamnati ta ambata
  • Gwamnati ta ce an sanya dokar ne a yau, kuma za ta fara aiki nan take domin shawo kan lamurra a yankin

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar hana fita hana fita a kananan hukumomin Jema’a da Kaura biyo bayan samun bayanai na shawari daga hukumomin tsaro na jihar.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta shafinta na Twitter.

Dokar hana fita a Jema'a da Kura
Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana fita a yankuna 3 na jihar | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Sanarwar ta ce:

"Biyo bayan shawarwarin hukumomin tsaro, KDSG ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jema’a da Kaura tare da fara aiki nan take. Hakan na nufin taimakawa jami’an tsaro wajen daidaita al’amura a yankunan, da ceton rayuka da dukiyoyi da kuma ba da damar maido da doka da oda."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: EFCC ta gano jami'in da ya yada bidiyon gwamna Obiano, za ta ladabtar dashi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatin jihar ta kuma bukaci daukacin mazauna yankunan da abin ya shafa da su bi umarnin hukumomi har sai an samu zaman lafiya a yankunan.

Idan baku manta ba, a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris, an kashe mutane akalla 15 a wani hari da wasu da ake zargin Fulani ne suka kai a Kagoro.

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

A wani labarin, kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) ta yi kira ga gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya ajiye girman kai sannan ya yarda cewa ya gaza magance kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma ayyukan ta’addanci da ke gudana a jihar, Daily Trust ta rahoto.

Shugaban CAN reshen jihar Kaduna, Reverend John Joseph Hayab, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, 21 ga watan Maris, inda ya fadama El-Rufai da tawagarsa da su mayar da hankali kan yakin da ceto jihar domin a tuna da shi a alkhairi bayan ya bar mulki.

Kara karanta wannan

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

Jawabin CAN na zuwa ne a daidai lokacin da aka karya doka da oda a yankin kudancin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel