Ke ce addu'a ta da aka karba: Hanan Buhari da Muhammad Turad sun shekara 1 da aure

Ke ce addu'a ta da aka karba: Hanan Buhari da Muhammad Turad sun shekara 1 da aure

  • Hanan Buhari da mijinta Muhammad Turad Sha'aban sun cika shekara cif da aure
  • Cike da shaukin kaunar matarsa, Turad ya wallaf cewa ita ce addu'arsa da aka amsa
  • Ba tare da bata lokaci ba, hazikar mai daukar hoton ta wallafa hotunansu tare da murna

Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Hanan Buhari da mijin ta, Muhammad Turad Sha'aban sun yi murnar cikarsu shekara daya cif da aure a ranar Asabar, 4 ga watan Satumba.

Hazikar mai daukar hoton tare da mijinta sun garzaya shafukansu na Instagram inda suka taya juna murnar cika shekara 1 da aure.

Allah ya amsa addu'ar da na dade ina yi, Hanan Buhari da Muhammad Turad sun shekara 1 da aure
Hoton Hanan Buhari da mijin ta, Muhammad Turad Sha'aban. Hoto daga @arewafamilyweddings
Asali: Instagram
"Ke ce addu'a ta da aka ansa! Ina mana murnar zagoyar ranar auren mu" Mohammed ya wallafa yayin da ya hada da kyakyawan hotonsu tare.

Kara karanta wannan

Buhari ya nada ni minista bayan sa'o'i 2 da karbar takardu na, Korarren minista Mamman

A bangaren ta, Hanan ta wallafa hotonsu a shafin ta na Instagram tare inda ta ce: "Murnar shekara 1 masoyi na."

Buhari ya nada ni minista bayan sa'o'i 2 da karbar takardu na, Korarren minista Mamman

A wani labari na daban, tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman ya bayyana yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a minista bayan ganin takardun sa bai wuci da sa’o’i biyu ba.

Daily Nigerian ta ruwaito hakan ne bayan kwanaki kadan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami ministan wutan lantarkin da kuma ministan ayyukan noma.

“Zan cigaba da yi wa shugaban kasa godiya saboda zabe na da yayi ba tare da na roke shi ba. Bai kai sa’a biyu ba da ya amshi takardu na ya nada ni a matsayin minista,” a cewar tsohon ministan.

Kara karanta wannan

Ba zan daina goyon bayan Shugaba Buhari ba, Korarren Ministar Lantarki Saleh Mamman

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng