Game da mulkin Buhari: Ku yi hakuri, ku yi ta addu’a, Gwamna Badaru ga ‘yan Najeriya

Game da mulkin Buhari: Ku yi hakuri, ku yi ta addu’a, Gwamna Badaru ga ‘yan Najeriya

  • Gwamnan jihar Jigawa ya bayyana yadda gwamnatin baya suka bar wa Buhari ayyuka barkate da ba a kammala ba
  • Ya bayyana cewa, kalubalen da kasar ke fuskanta ba a zamanin shugaba Buhari suka faro ba ko kadan
  • Ya ce, 'yan Najeriya su dage da addu'a idan suna son ganin sauyi na gari a Najeriya da kuma farfadowar kasar

Jigawa - Mohammad Badaru, gwamnan jihar Jigawa, ya bayyana yadda gwamnatin baya ta dagula kasar nan kafin daga bisani a mika mulki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, Gwamnan ya bayyana karara cewa, rashin tsaro da sauran kalubalen kasar nan ba a mulkin shugaba Buhari suka faro ba.

Kara karanta wannan

Tambuwal: Lamarin Buhari da Najeriya tamkar auren dole ne tsakanin namiji da mace

Badaru ya magantu kan batun kasar nan
Dama a dagule aka ba Buhari ragamar mulkin Najeriya, gwamna Badaru ya fadi dalili | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Gwamnan ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta samu ci gaba mai yawa musamman a bangaren ababen more rayuwa.

Badaru ya bayyana haka ne a jiya Lahadi a wajen bikin cika shekaru 60 da kafa kungiyar masu gabatar da shirye-shiryen gidajen radiyo ta Najeriya a birnin Dutse.

Ya ce akwai bukatar ‘yan Najeriya su yi hakuri da dagewa da addu’a domin kawo karshen kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da ke addabar al’umma.

Da yake tuna yadda gwamnatin baya ta barwa Buhari ayyuka barkate, gwamnan ya ce:

“Hanyoyi da ayyuka da dama da gwamnatocin da suka shude suka yi watsi da su wannan gwamnatin ta kammala su, yayin da wasu kuma ke gab da kammaluwa."

Ku dage da addu'a

Ya kuma bukaci 'yan Najeriya da su dage da addu'a domin ganin abubuwa sun sauya a kasar nan, Pulse ta tattaro yana cewa:

Kara karanta wannan

Aiki kai tsaye ga masu 1st Class: Majalisa ta tattauna kan daukar masu digiri aiki

“Najeriya na cikin wani mawuyacin hali kuma Allah Madaukakin Sarki ne ya yi alkawarin jarraba mu. Amma idan muka yi hakuri da dagewa da addu'a, to shi (Allah) zai kawo mana mafi alheri.
“Don haka ina rokon ku da ku yi hakuri kuma ku yi ta addu’a sosai, nan ba da jimawa ba Najeriya za ta murmure.
“Kuma duk da cewa kasar ba ta samu ci gaba a wasu bangarori ba, amma ta samu ci gaba sosai musamman a bangaren ababen more rayuwa. Domin ko da kuwa titin Kwanar Huguma – Shuwari – Azare – Damaturu gwamnatin Buhari ce ta kammala su.
“Kuma duk wadannan kalubale da suka hada da na tsaro da ku dasu, wannan gwamnati ta gada ne, amma muna yin iya bakin kokarinmu kuma za mu ci gaba da yin haka har sai Najeriya ta sake farfadowa. Amma wannan yana bukatar hakuri da addu’a”.

2023: Saraki, Tambuwal da ‘Yan takaran Arewa za su hada kai, domin tsaida mutum 1 a PDP

Kara karanta wannan

2023: El'rufai ya umurci kwamishina ya ajiye aiki bisa saboda sha'awar kujerar gwamna

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da wasu gwamnonin PDP biyu za su yi kokarin ganin an samu hadin-kai a zaben fitar da 'dan takara.

Daily Trust ta fitar da wani rahoto a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris 2022 inda aka ji cewa Bukola Saraki da Aminu Tambuwal sun ziyarci gwamnan Bauchi.

‘Yan siyasar sun tattauna da Sanata Bala Mohammed wanda yana cikin masu neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayyaa ta PDP a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel