Tambuwal: Lamarin Buhari da Najeriya tamkar auren dole ne tsakanin namiji da mace

Tambuwal: Lamarin Buhari da Najeriya tamkar auren dole ne tsakanin namiji da mace

  • Gwamna Aminu Tambuwal ya misalta dangantakar da ke tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari da Najeriya tamkar na auren dole tsakanin namiji da mace
  • Tambuwal ya ce Buhari bai fahimci yadda ake tafiyar da shugabanci irin na zamani ba
  • Ya kuma ce Najeriya na bukatar shugaba wanda ya fahimce ta kuma wanda zai iya samar da daidaito kan muhimman al'amuran da suka shafi kasar

Kaduna - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai fahimci yadda ake tafiyar da shugabancin zamani ba.

Tambuwal a ranar Asabar, 19 ga watan Maris, ya ce alakar da ke tsakanin shugaban kasar da Najeriya tamkar ‘auren dole’ ne, jaridar The Cable ta rahoto.

Tambuwal: Lamarin Buhari da Najeriya tamkar auren dole ne tsakanin namiji da mace
Tambuwal: Lamarin Buhari da Najeriya tamkar auren dole ne tsakanin namiji da mace Hoto: PM News
Asali: UGC

Da yake magana a sakatariyar Peoples Democratic Party (PDP) a Kaduna, gwamnan na jihar Sokoto ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC da lalata kasar, Thisday ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tambuwal ne zai iya dinke barakar rashin jituwa tsakanin 'yan Arewa da Kudu, dan majalisa

Tambuwal ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun ga cewa APC ba ta iya ba kuma ba za ta iya kula da harkokinsu a matsayin jam’iyya ba. Ta yaya za ta iya samar da mulki da shugabancin kasa mai girma da wuyan sha’ani kamar Najeriya? Mun san rikicin APC a yau.
“Na fadi wannan a wani wajan kuma zan maimaita, lamarin shugaban kasa Muhammadu Buhari da Najeriya tamkar auren dole ne tsakanin namiji da mace.
“Da wuya a samu fahimta ko zaman lafiya. Shugaban kasar bai fahimci Najeriya da yadda ake tafiyar da shugabancin zamani ba.”

Tambuwal ya ce Najeriya na bukatar shugaba wanda ya fahimci kasar kuma wanda zai iya samar da daidaito kan muhimman al'amuran da suka shafi kasa.

“Domin ganin mun magance matsalolin Najeriya a yau, akwai bukatar mu samu babban jagoran kasar nan mutumin da ya fahimci Najeriya da kanta. Wadanda ke da abokai a duk wani lungu da sako na kasar nan.

Kara karanta wannan

Gwamna Aminu Tambuwal ya ba matasa satar amsar wanda za su marawa baya a 2023

“Za su iya tuntuba sannan su dauki hukuncin bai daya kan lamuran da suka shafi mutanen kasar nan. Za ka iya aikata hakan ne kawai idan kana da hanyar sadarwar da ake bukata.
“Muna bukatar mutum da zai iya hada kan kasar nan. Mutum da ya ke tsantsar dan Najeriya. Wanda ya fahimci yanayin shugabanci na zamani.”

Tambuwal ne zai iya dinke barakar rashin jituwa tsakanin 'yan Arewa da Kudu, dan majalisa

A wani labarin, tsohon dan majalisar wakilai, Yemi Arokodare ya roki yan Najeriya da su baiwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal damar shugabantar kasar da kawo sauye-sauye don inganta kasar.

Arokodare, wanda ya kasance a majalisar wakilai daga 2003 zuwa 2007 kuma shugaban kwamitin majalisar kan labarai, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a Abuja a ranar Alhamis, 17 ga watan Maris, Vanguard ta rahoto.

Ya ce: “Tambuwal na da jajaircewar shugabanci, Kankan da kai da kuma juriya don sauya fasalin kasar, gyara ta da kuma ceto ta.”

Kara karanta wannan

2023: El'rufai ya umurci kwamishina ya ajiye aiki bisa saboda sha'awar kujerar gwamna

Asali: Legit.ng

Online view pixel