Kotu Ta Ɗaure Wani Ɗalibi a Gidan Yari Saboda Ya Saci Taliya Da Indomi

Kotu Ta Ɗaure Wani Ɗalibi a Gidan Yari Saboda Ya Saci Taliya Da Indomi

  • Babbar kotun Gwagwalada da ke Abuja, a ranar Alhamis ta daure wani dalibi mai shekaru 19, Hillary Yunana a gidan gyaran hali
  • Alkalin ya daure shi watanni 4 ne bayan ya amsa laifin sa na balle wani shago inda ya saci taliya da indomi, da kuma kudi
  • Alkalin ya ba shi zabi akan ko dai ya biya N10,000 ga ko wanne cikin laifuka biyu da aka tuhume shi da su ko kuma ya kwashe watanni 4 a gidan yari

Abuja - A ranar Alhamis, babbar kotun shari’a ta Gwagwalada da ke Abuja ta yanke wa wani dalibi mai shekaru 19, Hillary Yunana, watanni 4 a gidan gyaran hali akan satar taliya da indomi daga wani shago.

An tuhumi matashin wanda mazaunin kauyen Bassa ne da ke kan titin jirgin sama a Abuja da laifin balle shago da kuma sata, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Cin mutuncin Daurawa da 'yar Kannywood ta yi: Na yafe wa Nafisa Ishaq, inji Sheikh Daurawa

Kotu Ta Ɗaure Wani Ɗalibi a Gidan Yari Saboda Ya Saci Taliya Da Indomi
Kotu Ta Ɗaure Wani Ɗalibi a Gidan Yari Saboda Ya Saci Taliya. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Alkali Sani Umar ya yanke masa hukunci ne bayan ya amsa laifukan da ake tuhumar sa da aikatawa sannan ya nemi rangwame.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkali Umar ya ba matashin zabi akan ko dai ya biya N10,000 ga ko wanne laifi da ya yi ko kuma ya yi zaman gidan yari na wata bibbiyu ga ko wanne cikin laifukan sa guda biyu.

A cewarsa, zai yi zaman gidan yarin ne dodar inda ya shawarce shi da kiyaye aikata makamancin wadannan laifukan nan gaba.

Matashin ya saci taliya guda 7, indomi 5 da kuma N10,000

Alkalin kamar yadda Vanguard ta bayana ya ce wannan hukuncin zai zama izina ga duk wadanda suke tunanin aikata makamancin hakan.

Tun farko lauyan mai kara, Abdullahi Tanko ya sanar da kotu yadda matashin ya balle sannan ya afka shagon Gift Ugochukwu a ranar 4 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Ya Kamata Buhari Ya Miƙa Wa Mulki, In Ji Matasan Arewa

Tanko ya ce saurayin ya saci taliya guda bakwai da kuma indomi guda biyar tare da kudi N10,000, gaba daya komai na N13,000.

A cewarsa, laifin ya saba da sashi na 346 da 287 na dokar Penal Code.

Kano: An cafke mai wankin mota da ya tsere da motar kwastoma ta N8.5m zuwa Katsina

A wani labarin, an kama wani mai aiki a wurin wankin mota a Kano, Abdullahi Sabo, saboda tsere wa da motar kwastoma da aka kawo masa wanki, Premium Times ta ruwaito.

Mai magana da yawun yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Daura, Jihar Katsina da motar na sata.

Mr Kiyawa ya ce, a ranar 30 ga watan Nuwamba, yan sanda sun samu korafi daga wata mazauniyar Badawa Quaters a Kano inda ta ce wani mai aiki a wurin wankin mota ya gudu masa da motarsa Honda Accord ta shekarar 2017.

Asali: Legit.ng

Online view pixel