Cin mutuncin Daurawa da 'yar Kannywood ta yi: Na yafe wa Nafisa Ishaq, inji Sheikh Daurawa

Cin mutuncin Daurawa da 'yar Kannywood ta yi: Na yafe wa Nafisa Ishaq, inji Sheikh Daurawa

  • Shiekh Aminu Daurawa ya yi martani a kan wa'azinsa da ya haddasa cece-kuce a baya-bayan nan
  • Malamin ya bayyana cewa wa'azin ba batsa bane sannan kuma cewa ba a yi sa don cin zarafi ko mutuncin wani ba
  • Daurawa ya kuma jadadda cewar ya yafewa budurwar da aka ce ta zage shi a kan haka

Shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Shiekh Aminu Daurawa, ya magantu a kan wa'azinsa da ya haddasa cece-kuce a kwanan nan.

Daurawa ya bayyana cewa bai yi wa'azin domin cin zarafi ko mutuncin wani ba, ya ce wa'azi ne da aka yi domin jan hankalin al'umma a kan duniya da kuma rudin da ke cikinta.

Hakazalika ya ce babu batsa a cikin kalamansa domin bayani ne ya dauko wanda Sayyidina Ali ya yi.

Kara karanta wannan

A kan bashin N2.7m da ta ke bin sa, magidanci ya nada wa matarsa mai juna biyu dukan mutuwa

Cin mutuncin Daurawa da 'yar Kannywood ta yi: Na yafe wa Nafisa Ishaq, inji Sheikh Daurawa
Cin mutuncin Daurawa da 'yar Kannywood ta yi: Na yafe wa Nafisa Ishaq, inji Sheikh Daurawa Hoto: duniyarlabarai.com
Asali: UGC

A cikin wani bidiyo da muryar Amurka ta wallafa, Daurawa ya kuma ce ya yafewa budurwar da aka ce ta zage shi kan haka tun ma kafin ta nemi yafiyarsa.

"Ban so na yi magana a kan wannan matsala ba saboda gani nake yi kamar ta wuce. Toh amma abubuwa guda uku ne zai sa dole nayi magana a kai kamar yadda yan uwa suka bukata.

"Na farko shine a cikin karatun da nayi ba inda aka yi batsa, babu kuma inda aka ci zarafin kowa. Karatu ne a kan duniya, malamai suna so su fadakar da mutane a kan duniya da yadda take halakar da mutane da zubar da jini, da ta’addanci, da kashe-kashe, da garkuwa da mutane, da kashe kananan yara duk ana yi ne saboda duniya.

Kara karanta wannan

Yankin Yarbawa zai balle daga Najeriya ba tare da bindiga ba, Sunday Igboho

"Sai malamai suka tashi su bayyanawa mutane duniya da yadda take da kuma illar shagala da duniya har a kai ana zubar da jini a kai. Don haka Sayyidina Ali shi ya yi wannan bayani ni kuma na dauko shi a cikin wannan tafisiri kurtubi. Kuma duk malamai sun gani a cikin tafsirin suratul Hadid, don haka ba batsa bane, ba cin fuska bane.

"Manyan malaman supaye sun kawo litattafansu, manyan malama ahlu sunnah ma sun kawo, manyan malaman shi’a suma sun kawo litattafansu, saboda haka ba batsa, ba a kuma yi wannan karatu don cin zarafin wani ba ko cin mutuncin wani.

"Na biyu, daga baya ake gaya mun wani bidiyo yana ta yawo wata ta zage ni, kamar yadda mutane suka gaya mun kuma daga baya aka ce ta bayar da hakuri. Toh ni kafin ma ta bayar da hakurin na yafe mata. Saboda ni a matsayina na me wa’azi akwai zagi, akwai suka, akwa yabo. Sama da shekara 30 da nake wa’azi na, na ji kalamai masu dadi, na kuma ji kalamai marasa dadi kuma basa damuna."

Kara karanta wannan

Ta Kacame: Mai Garkuwa Ya Yi Ƙorafi a Kotu, Ya Ce Abokansa Sun Cuce Shi Sun Bashi N200,000 Kacal Cikin N12m Da Suka Samu

Kalli bidiyon a kasa:

Farji ne mafi muni a jikin mace: Ba fadin Daurawa bane, na Sayyidina Ali ne, inji Dr Mansur Sokoto

A baya mun ji cewa gawurtaccen malamin nan mazaunin jihar Sokoto, Dr Mansur Ibrahim Sokoto ya yi karin haske kan wa'azin na Sheikh Darurawa, inda yace ba Daurawa bane ya fara fadin wannan magana.

Malamin ya ambaci littafin wani babban malamin tafsirin al-Kur'ani, kuma mabiyin mazahabar Malikiyya dan kasar Andalus, inda malamin ya nakalto wata maganar sahabin Annabi (SAW) kuma surukinsa; Sayyidina Ali (RA) cewa shi ya fadi cewa farjin mace ne mafi muni a jikinta.

Dr Mansur Sokoto dai ya fadi haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya rubuta ruwayar maganar Sayyidina Ali (RA) cikin harshen Larabci, kana ya fassara zuwa Hausa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel