Batanci ga Annabi: Kotun Musulunci a Kano Zata Yanke Hukunci Kan Bukatar Sheikh Abduljabbar

Batanci ga Annabi: Kotun Musulunci a Kano Zata Yanke Hukunci Kan Bukatar Sheikh Abduljabbar

  • Babbar Kotun Musulunci a Kano dake sauraron karar Abduljabbar ta sa ranar yanke hukunci kan bukatar ba da beli
  • Alkalin Kotun ya sanya ranar 31 ga watan Maris, 2022 domin bayyana matsayar Kotu kan bukatar bayan sauraron ɓangarorin biyu
  • Malamin ta hannun lauyansa, ya ɗau alkawarin cika duk wasu sharuɗɗa da Kotu zata gindaya masa

Kano - Babbar Kotun Musulunci dake zamanta a jihar Kano ta sanya ranar 31 ga watan Maris, 2022, domin yanke hukunci kan bukatar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Aminiya ta rahoto cewa Shehin Malamin ta hannun lauyansa, ya nemi Kotu ta ba da belinsa tare da alƙawarin zai yi biyayya ga dukkan sharuɗɗan da ta gindaya masa.

Abduljabbar Kabara
Batanci ga Annabi: Kotun Musulunci a Kano Zata Yanke Hukunci Kan Bukatar Sheikh Abduljabbar Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

Gwamnatin Kano ta gurfanar Sheikh Abduljabbar ne bisa zargin batanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) da kuma tunzura al'umma.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ya diro Najeriya daga Dubai, ya yi jawabi kan abinda ya faru bayan ya karbi ragamar APC

Yayin da yake gabatar da bukatar wanda yake kare wa a zaman Kotu, Lauyan Malamin ya yi alƙawarin cewa za su bi duk wasu sharuɗɗa da Kotu ta kafa musu.

Gwamnatin Kano ba ta yarda ba

Sai dai a ɓangaren masu shigar ƙara bisa jagorancin Lauya, Barista Sa'id Suraj, ya roki Kotu ta yi watsi da lamarin belin duba da girman laifin da ake tuhumarsa.

A cewarsa, babban laifin dake wuyan wanda ake ƙara ka iya kaiwa ga yanke masa hukuncin kisa matuƙar aka gano ya aikata karkashin dokar manyan laifuka ta Kano ACJL 171 (1).

A jawabinsa, Lauyan masu shigar da ƙara ya ce:

"Baya ga haka, a halin da ake ciki da ake kan gabar kariya babu wani dalili da za'a nemi belin wanda ake ƙara, kuma ba su bayyana wani dalili mai ƙarfi da zai sa Kotu ta ba da belinsa ba."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari Kaduna, sun tattara maza da mata 47

Sai dai a ɗaya ɓangaren Lauyan Malam Abduljabbar, ya ce Kotu na da ikon ba da belin wanda ake zargi kasancewar har yanzun ba'a tabbatar ya aikata laifin ba.

Wane mataki Kotu ta ɗauka kan haka?

Bayan wannan muhawara tsakanin bangarorin biyu, Alkalin Kotun Mai Shari'a, Sarki Yola, ya ɗage zaman zuwa 31 ga watan Maris, domin jin matsayar Kotu kan batun ba da belin.

A wani labarin na daban kuma Tsohon mataimakin gwamna ya fice daga APC, ya bi sahun Kwankwaso zuwa NNPP

Tsohon Mataimakin gwamna a Adamawa, ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa NNPP mai kayan marmari.

Sa'ad Tahir, ya koma jam'i'iyyar APC a 2018 domin ba da gudummuwarsa, yanzu kuma ya koma NNPP don kara wa demokaradiyya karfi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel