Gwamna Buni ya diro Najeriya daga Dubai, ya yi jawabi bayan karban ragamar APC

Gwamna Buni ya diro Najeriya daga Dubai, ya yi jawabi bayan karban ragamar APC

  • Shugaban APC na rikon kwarya kuma gwamnan Yobe, Mala Buni, ya dawo Najeriya kuma ya karɓi ramagar APC
  • Gwamnan ya yaba da halin dattako da shugaba Buhari ya nuna, sannan ya yaba aikin gwamnan Neja da ya wakilce shi
  • Ya roki manyan masu ruwa da tsaki da mambobi sun haɗa kan su domin nasarar jam'iyya a duk abinda ta sa gaba

Abuja - Gwamnan Mai Mala Buni na jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa ya dawo gida Najeriya bayan duba lafiyarsa a Dubai.

Gwamna Buni ya diro Najeriya ne ranar Alhamis 17 ga watan Maris, 2022, kuma ya karɓi ragamar jagorancin jam'iyyar APC.

Daraktan watsa labarai na gwamnan Yobe, Mamman Muhammed, shi ne ya sanar da dawowar Buni a wata sanarwa da aka fitar a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamna Buni ya yi amai ya lashe, ya amince da abubuwan da Bello ya zartas a APC

Gwamna Buni da Gwamna Bello
Gwamna Buni ya diro Najeriya daga Dubai, ya yi jawabi bayan karban ragamar APC Hoto: Mamman Mohammed/facebook
Asali: Facebook

A sanarwan, Buni ya roki masu ruwa da tsaki da mambobi su tallafa wa jam'iyya yayin da take shirye-shiryen gudanar da babban taronta ranar 26 ga watan Maris.

Hakanan shugaban kwamitin rikon kwarya ya kuma bukace su da su jingine duk wani saɓani da ka iya zama barazana ga samun nasarar APC.

Buni ya ce:

"Yayin da muke fuskantar babban taron jam'iyyar mu ta APC, kauna da goyon bayan kowane mamba da masu faɗa aji na da matuƙar muhimmanci. Ƙarfin mu shine haɗin kan mu a ɗai-ɗaiku da ƙungiyance."
"A matsayin mu na yan demokaraɗiyya da jajirtattun mambobi, ya kamata mu guji abubuwan da zasu ɗauke hankulan mu daga hanyar nasara."

Buni ya yaba wa Buhari da gwamna Bello

Bugu da ƙari, Mala Buni ya ce babbar ni'imar da Allah ya yiwa APC shi ne samun shugaba Buhari a matsayin jagora, wan da a kafaɗara jam'iyya ke rawa ta ɗaka tsalle har ta samu nasara.

Kara karanta wannan

Labarin cikin Hotuna: Mai Mala Buni yayi takakkiya zuwa Landan don ganin Shugaba Buhari

"Abubuwa da dama sun wakana a kwanakin nan, haka kowace jam'iyya ke fuskanta duk lokacin da take kan siraɗin cigaba da nasara. Abun da ya fi muhimmanci shi ne sauke nauyi da cimma manufa."
"Na yaba sosai da rawar da gwamnan Neja, Abubakar Bello, ya taka a madadi na kuma ya tafiyar da harkokin jam'iyya lokacin da bana kusa. Duk matakin da ya ɗauka tankar ni na zartas."

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta bayyana yan majalisu 14 da zata baiwa tikitin takara kai tsaye a 2023

Gabanin zaben 2023 dake tafe, jam'iyyar APC reshen jihar Edo ta fara shirye-shiryen kawar da PDP daga mulkin jihar.

Duk da sauya shekar gwamna mai ci zuwa tsagin hamayya PDP, cikin kwarin guiwa APC tace zata lashe kujerun yan majalisu baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel