Daga karshe: An rantsar da dan jam'iyyar APGA a matsayin gwamnan Anambra

Daga karshe: An rantsar da dan jam'iyyar APGA a matsayin gwamnan Anambra

  • Gwamnati da mutanen Anambra a ranar Alhamis, 17 ga watan Maris, sun samu sabon shugaba wato Farfesa Charles Chukwuma Soludo
  • Soludo, har zuwa lokacin da aka rantsar da shi a ranar Alhamis a Akwa, babban birnin jihar, shi ne zababben gwamnan jihar bayan kada kuri'a a watan Nuwamban bara
  • Bikin rantsarwar, kamar yadda majiyoyi suka bayyana, ya samu halartar jiga-jigan 'yan Najeriya 50 da ‘yan jarida kadan

Zababben gwamnan Anambra, Charles Chukwuma Soludo, ya karbi ragamar mulkin jihar a matsayin sabon shugabanta.

Soludo wanda ya karbi ragamar mulki daga hannun magabacinsa, Wilie Obiano, an rantsar da shi a matsayin gwamna a ranar Alhamis, 17 ga watan Maris, in ji jaridar New Telegraph.

An rantsar da Soludo a matsayin gwamnan Anambra
Daga karshe: An rantsar da dan jam'iyyar APGA a matsayin gwamnan Anambra | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Soludo, wanda ya taba rike gwamnan babban bankin Najeriya ya yi takara a jam'iyyar APGA ne.

Kara karanta wannan

'Karin Bayan: Soludo Ya Yi Magana Kan Marin Da Matar Obiano Ta Yi Wa Bianca Ojukwu a Wurin Taron Rantsar Da Shi

Soludo ya lashe zaben gwamnan Anambra da kuri'u 112,229, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bankwana

Channels Tv ta ruwaito cewa, kwanaki dai tsohon gwamnan ya mikawa sabon gwamnan wasu takardun tafiyar da jihar.

A jawabinsa na bankwana, Obiano ya godewa jihar bisa gata da ta bashi na yi mata hidima, inda ya nemi gafarar wadanda ya yiwa ba daidai ba. Ya kuma ce shi bai da mugun nufi kan kowa.

Matar tsohon gwamna Obiano ta shararawa Bianca Ojukwu mari a wajen rantsar da Soludo

A wani labarin, an yi takaddama a ranar Alhamis yayin da aka rantsar da Farfesa Charles Soludo a matsayin gwamna inda matar Willie Obiano Ebelechukwu da Bianca Ojukwu suka kaure da fada, inji rahoton The Nation.

Matar Obiano ta gaurawa Bianca mari, inda ta zarge ta da cewa ba ta son mijinta ya zama Gwamna yayin da ta kira ta yar iska.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Matar tsohon gwamna Obiano ta shararawa Bianca Ojukwu mari a wajen rantsar da Soludo

Cikin fusata da bacin rai, Mrs Ojukwu ta mike ta mari matar Obiano, lamarin da ya kai ga fada tsakaninsu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel