Soludo Ya Yi Magana Kan Marin Da Matar Obiano Ta Yi Wa Bianca Ojukwu a Wurin Taron Rantsar Da Shi

Soludo Ya Yi Magana Kan Marin Da Matar Obiano Ta Yi Wa Bianca Ojukwu a Wurin Taron Rantsar Da Shi

  • Farfesa Charles Soludo, gwamnan Jihar Anambra ya nuna damuwarsa kan fadar da aka yi tsakanin matar gwamna mai barin gado, Ebele Obiano da Bianca Ojukwu.
  • Soludo ya ce jiharsa wuri ne na cigaba da kuma bin doka da oda, ya kara da cewa duk wanda bai son hakan yana iya tafiyarsa
  • Soludo ya rattaba hannu kan takardun ne a gaban babban alkalin Jihar Anambra, Mai Sharia Onochie Anyachebelu da wasu mazauna jihar da suka hallarci taron

Anambra - Charles Soludo, zababben gwamnan Jihar Anambra da aka rantsar a ranar Alhamis 17 ga watan Maris na 2022 ya nuna damuwarsa kan musayar maganganu da mari da aka yi tsakanin matar gwamna mai barin gado, Ebele Obiano da Bianca Ojukwu.

Kara karanta wannan

Karfin hali: Matar tsohon gwamna Obiano ta shararawa Bianca Ojukwu mari a wajen rantsar da Soludo

Da ya ke magana minutuna bayan afkuwar lamarin, Soludo, wanda ya mayar da hankali wurin rattaba hannu kan takardun rantsar da shi ya ce wadanda ke son barin wurin suna iya tafi, rahoton Vanguard.

Yanzu-Yanzu: Soludo Ya Yi Magana Kan Marin Da Matar Obiano Ta Yi Wa Bianca Ojukwu a Wurin Taron Rantsar Da Shi
Soludo Ya Yi Magana Kan Marin Da Matar Obiano Ta Yi Wa Bianca Ojukwu a Wurin Taron Rantsar Da Shi. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Soludo ya rattaba hannu kan takardun ne a gaban babban alkalin Jihar Anambra, Mai Sharia Onochie Anyachebelu da wasu mazauna jihar da suka hallarci taron.

Sabon gwamnan da aka nada ya sanar da mutanen Anambra cewa jihar ta mayar da hankali ne wurin cigaba kuma jiha ce wacce ake bin doka da oda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalamansa:

"Wadanda suke son tafi suna iya tafiya. Anambra da muke magana a kai wuri ne na bin doka da oda.

A lokacin da ya ke jawabi, tsohon gwamna Wille Obiano da matarsa sun bar wurin taron rantsarwar, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Daga karshe: An rantsar da dan jam'iyyar APGA a matsayin gwamnan Anambra

Yadda abin ya faru

Tuda farko, Wani abu mai kama da dirama ya faru a wurin kaddamar da Farfesa Charles Soludo a matsayin gwamnan jihar Anambra a yayin da matar gwamna mai barin gado, Willie Obiano, Ebelechukwu, ta mari Mrs Bianca Ojukwu a wurin taron, rahoton Daily Trust.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ta bakin wakilinta da ke wurin taron ta rahoto cewa lamarin ya faru ne nan take bayan Solodu ya yi rantsuwar kama aiki.

NAN ta rahoto cewa manyan baki ciki har da tsohon gwamna Obiano sun riga sun zauna yayin da Mrs Obiano ta shigo ta wuce layin gaba inda tsohuwar matar na Dim Odumegwu Ojukwu ke zaune ta sharara mata mari.

Hakan ya janyo hankalin jami'an tsaro da wasu mutane da suka kwato Mrs Obiano daga hannun Bianca wacce bisa ga alamu ta yi mamakin abin da ya faru.

Daga bisani an tafi da Mrs Obiano daga wurin taron, shi ma mijinta ya bar wurin taron bayan afkuwar lamarin da kuma rantsar da sabon gwamnan.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel