A kan bashin N2.7m da ta ke bin sa, magidanci ya nada wa matarsa mai juna biyu dukan mutuwa

A kan bashin N2.7m da ta ke bin sa, magidanci ya nada wa matarsa mai juna biyu dukan mutuwa

  • Ana zargin matashin magidanci, MC Bonus Emmanuel Chigozie da nada wa matarsa dukan da yayi ajalinta da jaririn da ke cikinta
  • Majiya ta tabbatar da cewa yana kai mata farmaki ne a duk lokacin da ta bukaci ya biya ta N2.7 miliyan da ta ke binsa bashi
  • Bayan dukanta, an kai Itunu asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwar jinjirin cikinta kafin tace ga garin ku daga bisani

Legas - Ana zargin wani MC dan Najeriya mai suna Bonus Emmanuel Chigozie, da yi wa matarsa mai juna biyu, Itunu Lawal Emmanuel mugun dukan da yayi ajalinta.

Mummunan lamarin ya auku a gidansu da ke yankin Okota a jihar Legas kamar yadda shafin Instablog9ja ya ruwaito.

A kan bashin N2.7m da matarsa ke bin sa, magidanci ya nada wa matarsa mai juna biyu dukan mutuwa
A kan bashin N2.7m da matarsa ke bin sa, magidanci ya nada wa matarsa mai juna biyu dukan mutuwa. Hoto daga @instablog9ja
Asali: Instagram
Kamar yadda wata majiya ta sanar, "Sun yi aure shekaru hudu da suka gabata. Emmanuel ya fara dukan matarsa bayan sun yi haihuwar farko. Kwatsam ya zamo ya tsane ta kuma a kodayaushe neman dalilin da zai ci zarafinta yake yi.

Kara karanta wannan

Ta Kacame: Mai Garkuwa Ya Yi Ƙorafi a Kotu, Ya Ce Abokansa Sun Cuce Shi Sun Bashi N200,000 Kacal Cikin N12m Da Suka Samu

"Ya fara cin amanarta kuma budurwa da yake nema ta fara yi mata barazana matukar bata bar auren ba."

A cewar majiyar, ya cigaba da dukan Itunu kuma cin zarafin yana karuwa ne a duk lokacin da ta bukaci ya biya ta N2.7 miliyan da ta ranta masa.

A lokacin da ta samu juna biyu za ta haifa dan su na biyu, ya dinga dukanta har dan ya mutu a cikinta.

An gaggauta mika ta asibiti inda aka tabbatar da mutuwar jinjirin sannan tace ga garinku a ranar Alhamis, 10 ga watan Maris.

Emmanuel ya yi batan dabo a yayin da aka kwantar da ita a asibiti, amma ya bayyana bayan da aka sanar da shi mutuwar matarsa.

Wata majiya makusanciya ga marigayiyar ta ce:

Kara karanta wannan

Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce

"Tun a watan Disamba ta ke sanar da ni cewa tana tsoron za ta iya samun matsala da cikin saboda yadda mijinta ya dinga kai mata farmaki tare da dukan ta yayin da take da juna biyun."

Jama'a sun yi martani

Bayan wannan wallafa, jama'a sun dinga tofin Allah wadai ga wannan magidanci. Ga wasu daga cikin tsokacin mutane:

@iam.hendrixx cewa tayi: "Tunda kun kware a bugu, mai zai hana ku bar auren ku koma dambe?"
@priceless_cdf cewa yayi: "Rayuka 2 masu matukar muhimmanci aka rasa. Na san mutanen da ke cikin irin wannan hali. Don Allah ku yi kokarin gyarawa idan komai ba ya tafiya daidai. Tattara komatsan ki ki tsere idan ba za a iya zama ba."
@oochy_coochie tace: "Mata da yawa na shan bakar wahala don kawai su zauna da auren da tuni ya mutu."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel