Bidiyo ya bayyana: Bianca Ojukwu ce ta kaftawa matar gwamna mai barin gado Obiano mari

Bidiyo ya bayyana: Bianca Ojukwu ce ta kaftawa matar gwamna mai barin gado Obiano mari

  • Wani bidiyo ya bayyana gaskiyar yadda aka mari matar tsohon gwamna a filin rantsar da sabon gwamnan Anambra
  • Wannan lamari ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta kasancewar ba a taba tsammanin hakan ba
  • Daya baya gwamnan jihar na Anambra, Charles Soludo ya yi martani kan wannan lamarin mara dadi

Wani faifan bidiyo da ke yawo a Facebook ya bayyana cewa Bianca Ojukwu ce ta mari matar tsohon Gwamna Willie Obiano, Ebelechukwu, a wajen bikin rantsar da Charles Soludo a matsayin sabon gwamnan jihar Anambra, ba wai akasin haka ba.

Misis Ojukwu ita ce matar marigayi jagoran Biafra, Odumegwu Ojukwu, inji rahoton Premium Times.

Yadda matar gwamna ta sha mari
Bidiyo ya bayyana: Bianca Ojukwu ce ta kaftawa matar gwamna barin gado Obiano mari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

Kasancewar Misis Obiano ce ta tashi daga kujerar ta zuwa inda Misis Ojukwu take zaune, mutane da dama ciki har da ‘yan jarida sun dauka Mrs Obiano ce ta fara kai marin.

Kara karanta wannan

'Karin Bayan: Soludo Ya Yi Magana Kan Marin Da Matar Obiano Ta Yi Wa Bianca Ojukwu a Wurin Taron Rantsar Da Shi

Lamarin ya faru ne nan take bayan an rantsar da gwamna Soludo na jihar Anambra.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani dan jarida, Charles Ogbu, ya yi tsokaci game da faifan bidiyon da ya nuna hakikanin abin da ya faru, inda yace:

"Wannan wani karin bidiyo ne na bikin abin kunya da ya faru a yau a bikin rantsar da Gwamna Charles Chukwuma Soludo."
“A cikin wannan faifan bidiyon, uwargidan tsohon gwamnan jihar, Cif Willie Obiano, Osodieme Obiano, ta yi tattaki zuwa inda Bianca Odumegwu Ojukwu ke zaune.
"Kuma bayan cacar bakin da ba a ji ba, ana iya ganin Bianca na ba matar Obiano kyauta abin da mutane da yawa suka bayyana a matsayin marin kwana.”

Wata jarida ta yanar gizo ta ruwaito cewa Mrs Obiano ta yi wa Misis Ojukwu ba'a ne, tana mai cewa:

Kara karanta wannan

Karfin hali: Matar tsohon gwamna Obiano ta shararawa Bianca Ojukwu mari a wajen rantsar da Soludo

"Na dauka kin ce ba za mu taba yin gwamna ba."

Misis Ojukwu dai an ce ta sha nuna adawa da gwamnatin Gwamna Obiano a tsawon shekaru takwas da yayi.

Soludo Ya Yi Magana Kan Marin Da Matar Obiano Ta Yi Wa Bianca Ojukwu a Wurin Taron Rantsar Da Shi

Jim kadan bayan rikicin, Farfesa Charles Soludo, gwamnan Jihar Anambra ya nuna damuwarsa kan marin da matar gwamna mai barin gado, Elechekwu ta yi wa Bianca Ojukwu.

Ko da ya ke ya mayar da hankali wurin rattaba hannu kan takardun da alkalin alkalan jihar Mai Sharia Onochie Anyachebelu ya kawo masa. A yayin da ya fara jawabinsa, ya ce:

"Wadanda suke son su tafi za su iya tafiya.
"Jihar Anambra da muke magana a kai wuri ne na bin doka da oda."

Asali: Legit.ng

Online view pixel