Yayinda Buni ya koma mulkinsa na APC, INEC tace yanzu zata halarci taron NEC na APC

Yayinda Buni ya koma mulkinsa na APC, INEC tace yanzu zata halarci taron NEC na APC

  • Hukumar INEC ta bayyana cewa yanzu zata halarci taron NEC na APC idan Mai Mala ya rattafa hannu
  • Rahotanni sun nuna cewa Sakataren APC da sauran mabiyan Mai Mala sun mamaye sakatariyar jam'iyyar
  • Taron majalisar zartaswar APC zai gudana ta yanar gizo, Buni daga Dubai, Buhari daga Landan

Abuja - Hukumar gudanar da zabe INEC ta tabbatar da cewa zata halarci taron majalisar zartaswar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da za'ayi gobe Alhamis, 17 ga Maris, 2022.

Hukumar tace zata halarta idan APC ta sake aikewa da wasika dauke da rattafa hannun Shugabanta Mai Mala Buni da Sakatare, John James Akpanudoedehe.

Wannan ya biyo bayan komawar Gwamna Mala Mai Buni mulkin na APC kuma mabiyansa sun kwace hedkwatar jam'iyyar.

Hukumar INEC
Yayinda Buni ya koma mulkinsa na APC, INEC tace yanzu zata halarci taron NEC na APC Hoto: INEC
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tinubu zai gana da Sanatocin jam'iyyar APC a yau dinnan

Leadership ta ruwaito cewa ta samu ji cewa Mai Mala Buni zai jagoranci taron majalisar zartaswar ta yanar gizo saboda bai Najeriya yanzu kuma Shugaba Buhari ma zai yi musharaka daga Landan.

Rahoton ya kara da cewa kwamishanan yada labaran INEC, Festus Okoye, yace idan APC ta aike musu da wata wasikar dauke da sa hannun Mai Mala Buni da Sakatare Akpanudoedehe, zasu halarci zaman.

Yace:

"Bamu da matsala da jam'iyyar. Matsayarmu itace su sanar da mu ana saura awanni 48 cewa suna son gudanar da taron majalisar zartaswa."
"Wajibi ne Shuggaban jam'iyyar da Sakatare su rattafa hannu Idan suka rubuto mana, zamu amsa gayyatar."

Taron gangamin APC: Shugaban jam'iyya da Sakataren jam'iyya basu sanya hannu ba - INEC

Hukumar zabe ta kasa INEC ta yi watsi da wasikar gayyata zuwa taron majalisar zartaswa na gaggawa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta bayyana yan majalisu 14 da zata baiwa tikitin takara kai tsaye a 2023

Hukumar INEC ta bayyana cewa ta yi watsi da takardar ne saboda bata ga sanya hannun Shugaban jam'iyya da na Sakatare AkpanUduohehe ba.

INEC, a wasikar da ta aike ranar 9 ga Maris, 2022 kuma Sakatarenta, Rose Oriaran Anthony, ta rattafa hannu, hukumar ta ce APC ta saba ka'idar Article 1.1.3 na dokokin ayyukan jam'iyyun siyasa.

INEC ta kara da cewa bisa sashe na 82(1) na dokar zabe, akwai bukatar a sanar da ita ana saura kwanaki 21 akalla kafin wani babban taro, ko ganawa don maja da zaben sabbin shugabanninta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel