Taron gangamin APC: Shugaban jam'iyya da Sakataren jam'iyya basu sanya hannu ba - INEC

Taron gangamin APC: Shugaban jam'iyya da Sakataren jam'iyya basu sanya hannu ba - INEC

  • Hukumar INEC ta watsawa jam'iyyar APC kasa a ido game da taron majalisar zartaswar da ta yi shirin yi
  • Duk da sabon shugaban APC ya rattafa hannu kan wasikar, INEC tace ita Mai Mala ta sani matsayin Shugaban APC
  • Wannan na faruwa ne ana saura kwanaki 16 taron zaben sabbin shugabannin jam'iyyar APC na kasa

FCT Abuja - Hukumar zabe ta kasa INEC ta yi watsi da wasikar gayyata zuwa taron majalisar zartaswa na gaggawa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Hukumar INEC ta bayyana cewa ta yi watsi da takardar ne saboda bata ga sanya hannun Shugaban jam'iyya da na Sakatare AkpanUduohehe ba.

Da yiwuwan yunkurin cire Mai Mala Buni karfi da yaji ya fuskanci babban matsala.

Wasikar INEC
Yanzu-yanzu: Mai Mala Buni muka sani, babu ruwanmu da wani sabon Shugaban APC - INEC Hoto: INEC
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jam'iyyar APC ta yiwa INEC raddi kan wasikar da ta aike mata

INEC, a wasikar da ta aike ranar 9 ga Maris, 2022 kuma Sakatarenta, Rose Oriaran Anthony, ta rattafa hannu, hukumar ta ce APC ta saba ka'idar Article 1.1.3 na dokokin ayyukan jam'iyyun siyasa.

INEC ta kara da cewa bisa sashe na 82(1) na dokar zabe, akwai bukatar a sanar da ita ana saura kwanaki 21 akalla kafin wani babban taro, ko ganawa don maja da zaben sabbin shugabanninta.

INEC ta bayyanawa APC cewa saboda haka tayi watsi da wasikar.

Wasikar tace:

"Hukumar na janyo hankalinku kan cewa Shugaban jam'iyya da Sakatare basu rattafa hannu kan zaman majalisar ba kuma wannan ya sabawa Article 1.1.3 na ka'idojin harkokin jam'iyyu (2018)."
"Baya haka, muna tunawa APC sashe na 82(1) na dokar zaben 2022 wanda ke bukatar sanar da hukumar kan wani taro, ganawa, ko zama don niyyar zaben shugabanni ana saura akalla kwanaki 21."

Jam'iyyar APC ta kira taron majalisar zartaswa na gaggawa ranar Alhamis

Kara karanta wannan

An tunawa ‘Yar Abiola abin da ta fada a 2018 a kan APC yayin da ta shirya tsayawa takara

Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta kira taron majalisar zartaswa na gaggawa ranar Alhamis, 17 ga watan Maris a hedkwatarta dake birnin tarayya Abuja.

Jam'iyyar ta gayyaci dukkan mambobin majalisar zartaswan a wasikar da ta saki da safiyar nan a shafinta na Tuwita.

Mambobin majalisar sun hada da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari; mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, dukkan Gwamnonin jam'iyyar APC, Sanatoci da sauran masu ruwa da tsaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel