Karin ilimi: Kwankwaso ya karo karatu, ya kammala digirin digirgir daga kasar India

Karin ilimi: Kwankwaso ya karo karatu, ya kammala digirin digirgir daga kasar India

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karo ilimi a kasar Indiya
  • Jami’ar Sharda ta kasar Indiya ce ta baiwa Kwankwaso digirin digirgir a fannin Injiniyan Ruwa
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook

Jami’ar Sharda ta kasar Indiya ta bai wa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso digirin digirgir a fannin Injiniyan Ruwa.

Kwankwaso a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Litinin, 14 ga watan Maris, ya yi godiya ga kansa a kan wannan nasara da ya samu.

Karin ilimi: Kwankwaso ya karo karatu, ya kammala digirin digirgir daga kasar India
Kwankwaso ya karo karatu, ya kammala digirin digirgir daga kasar India Hoto: Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso, FNSE
Asali: Facebook

Ya rubuta:

"Alhamdulillah, Muna taya mai Girma Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso murna bisa nasarar kammala karatun Digrin Digirgir (PhD) a fannin Kimiyya na Ruwa a Jami'ar Sharda dake India (14th March, 2022). A gefen damansa shine Farfesa Gaurav Saini (Mai duba karatunsa), daga hagu kuma Farfesa Rameshwar Adhikar (daga Jami'ar Tribhuwan a Kathandu Nepal) wanda ya duba karatunsa/binciken ilimi daga waje, tareda sauran Farfesa wanda suka halarci taron.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Muna taya mai Girma Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso gatan Ilimi murna."

‘Yan siyasa, musamman daga Kano ciki har da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, sun sha yin takama da irin nasarorin da suka samu a fannin ilimi, wanda ke nuna yadda suke gaban Kwankwaso a fannin ilimi.

Daily Trust ta rahoto cewa yan siyasa kamar kwamishinan ci gaban kakkara na jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, wanda ya fito daga gari guda da tsohon gwamnan kan yiwa matsayin karatun digiri digirgir na Kwankwaso ba’a, inda ya kan yi masa lakabi da ‘mai bracket’.

Babu wani aibu don mutum ya sauya sheka a siyasa - Kwankwaso

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa shi bai ga wani aibu ba don yan siyasa sun sauya sheka daga wata jam’iyya zuwa wata, cewa hakan wani tsari ne na siyasa.

Kwankwaso ya bayyana cewa akwai hikima sosai idan dan siyasa ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya domin gwada farin jininsa da kuma karbuwarsa a cikin mutane.

Dan siyasan ya bayyana hakan ne a Kano, a ranar Lahadi, 6 ga watan Maris, yayin wata ganawa da yan Kwankwasiyya da kuma jiga-jigan PDP a jihar a gidansa da ke Miller Road, Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel