Magidanci ya yasar da matarsa da 'ya'yansa a Najeriya, ya koma Spain da takardunsu

Magidanci ya yasar da matarsa da 'ya'yansa a Najeriya, ya koma Spain da takardunsu

  • Wata matar aure ta shiga cikin takaici bayan mijinta yayi watsi da ita da yaranta a Najeriya daga zuwa hutu
  • Mutumin ya dawo Najeriya da iyalinsa kamar yadda ya saba dawowa hutu, sai dai ya koma mazauninsu a kasar Spain da takardun tafiyar su
  • Matar mai zubda hawaye, yayin kokawa a kan halayyar mijintan na ban mamaki, ta dora laifin a kan yayar mijin

Iyalin da a halin yanzu suke cikin tsananin rudani bayan halayyar ban mamakin da jigon iyalin yayi. A da can iyalin suna rayuwa ne a Turai, amma a yanzu suna zaune a Najeriya, yayin da mijin ke zaune a kasar Spain.

Chinedu ya dauki iyalinsa zuwa Najeriya kamar yadda ya saba zuwa gida hutu.

Magidanci ya yasar da matarsa da 'ya'yansa a Najeriya, ya koma Spain da takardunsu
Magidanci ya yasar da matarsa da 'ya'yansa a Najeriya, ya koma Spain da takardunsu. Hoto daga TikTok/@favouritenews
Asali: UGC

An samu labarin yadda mijin, wanda shi ne jigon iyalin, mai suna Chinedu, ya dauko iyalinsa daga kasar Spain da suke zaune da sunan hutu zuwa gida Najeriya.

Kara karanta wannan

Katsina: Yan bindiga sun bude wuta a kan wata mota, sun kashe fasinjoji 5

Sai dai, ya koma Spain shi kadai da takardun tafiyar su, inda ya bar su a nan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani bidiyo da @favouritenews suka wallafa a TikTok na nuna yadda matarsa cikin kuka ta bayyana rashin jindadin halayyar mijinta, inda ta labarta yadda bata da masaniya a kan yadda yayi shirin watsi dasu a Najeriya.

Bayan nazari mai zurfi a a bidiyon, matar ta dora laifi akan yayar Chinedu, na canza mishi ra'ayi.

Hakan ya jawo cecekuce daga mutanen yanar gizo.

Khadijat Ifelewa Oritoke ta ce: "Watakila matar tayi kokarin jefa shi a matsala a can kasar ne, shi kuma mutumin baya son rasa aikinsa. Gaskiya na yaba da dabarar mutumin."
Famous Freedom ta ce: "Ni dai na dena saurarar labari daga bangare daya tun da jimawa, abu kadan sai mu fara dorawa wasu da ;yan kauye laifi, wani lokaci ya kamata mu binciki kawunan mu idan muna bin hanya mai kyau, kawai dai abunda da banso ba a nan, shine yadda ya maido su Najeriya, ya kamata a ce ya kaisu wani wurin ko watakila za su koya ko gyara laifinsu, Najeriya a halin yanzu jihannama ce."

Kara karanta wannan

Lawan, Goje, Amaechi Da Sauran Ƴan Siyasa 4 Da Ake Damawa Da Su Tun 1999

Goldenheart1999 ya ce: "Shawarata ga dukkan ku shi ne, kada ku yi makahon so kuma kada ku yarda da kowa. Ni ne na aje takardun a lokacin da muka kai ziyara gida."
Barbara William yayi tsokaci: "Wadanda ke cewa ta je ofishin jakadancin kasa, ku tuna zasu tambayeta inda mijinta yake ko kuma babu yadda yaran zasu iya tafiya."

Matan Saudi sun fara kabo-kabo da tasi yayin da tsadar rayuwa ta tsananta a kasar

A wani labari na daban, bayan tsanantar tsadar rayuwar jama'a mazauna kasar Saudi Arebiya, mata ma sun tashi tsaye wajen neman abun sawa a bakin salatinsu a fadin masarautar, punch ta ruwaito.

Kamar dai sauran matan Saudiya, Fahda Fahd ba ta samu lasisin tuki ba sai a shekarar 2018, sai dai a halin yanzu tana amfani da motar ta kirar KIA kalar koriya don neman 'yan canji, duba da irin tsadar rayuwar da masarautar ke ciki.

Kara karanta wannan

A kan bashin N2.7m da ta ke bin sa, magidanci ya nada wa matarsa mai juna biyu dukan mutuwa

A ranakun da ba ta zuwa aikin asibiti, tsohuwar mai shekaru 54 na kabo-kabo a babban birnin Riyadh daga tashar direbobi mata, The punch ta ruwaito. Fahd ta bayyana yadda iyalinta suka goyi bayan wannan aikin nata, bisa sharudda guda biyu: banda tafiya mai nisa ko daukar fasinjoji maza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel