Matan Saudi sun fara kabo-kabo da tasi yayin da tsadar rayuwa ta tsananta a kasar

Matan Saudi sun fara kabo-kabo da tasi yayin da tsadar rayuwa ta tsananta a kasar

Saudi Arabia - Bayan tsanantar tsadar rayuwar jama'a mazauna kasar Saudi Arebiya, mata ma sun tashi tsaye wajen neman abun sawa a bakin salatinsu a fadin masarautar, punch ta ruwaito.

Kamar dai sauran matan Saudiya, Fahda Fahd ba ta samu lasisin tuki ba sai a shekarar 2018, sai dai a halin yanzu tana amfani da motar ta kirar KIA kalar koriya don neman 'yan canji, duba da irin tsadar rayuwar da masarautar ke ciki.

Matan Saudi sun fara kabo-kabo da tasi yayin da tsadar rayuwa ta tsananta a kasar
Matan Saudi sun fara kabo-kabo da tasi yayin da tsadar rayuwa ta tsananta a kasar. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

A ranakun da ba ta zuwa aikin asibiti, tsohuwar mai shekaru 54 na kabo-kabo a babban birnin Riyadh daga tashar direbobi mata, The punch ta ruwaito.

Fahd ta bayyana yadda iyalinta suka goyi bayan wannan aikin nata, bisa sharudda guda biyu: banda tafiya mai nisa ko daukar fasinjoji maza.

"Na yanke shawarar aiki a matsayin direban tasi don samun abunda zan rufa wa kaina asiri," a cewar Fahd, wacce ke sanye da nikab da takunkumin fuska.

Kara karanta wannan

Yin arziki 'yan Crypto zai tabbata: Amurka ta juyo kan 'yan Crypto, za su ga canji nan kusa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Albashina ba ya isar yara na uku, musamman diya ta, wacce ke da bukatu daban da sauran," ta bayyana wa AFP

Fahd ta ce, tana samun riyal 4,000 ( $1,066) da take samu a duk karshen wata daga dayan aikin da take - amma kabo-kabo na kara kawo mata wata riyal 2,500.

Ta na bazama kan titi ne kafin karatowar lokacin aikin ta karfe 2;00 na rana, wani lokaci ta kan dauki fasinjoji a hanyarta na dawowa gida misalin karfe 10:00 na dare, inda ta ce tana matukar jin dadin aiwatar da al'amuranta cikin sauki.

"Hakan na bani damar taimaka wa mijina da yayi ritaya wajen biyan mishi bashi a duk karshen wata da bukatun makarantar yarana," a cewarta.

Samun sabuwar dama a rayuwa

Tsadar rayuwa na cigaba da tsananta a Saudi Arebiya, yayin da aka yi kokarin rage dogaro da man fetur a matsayin babban tattalin arzirkin kasar a watan Yuli 2020, an kara farashin kudin haraji zuwa 15 bisa dari na abunda ake biya a baya.

Kara karanta wannan

Shiga aikin soja: Abubuwa 5 kuke bukata domin shiga aikin sojin Najeriya

A shakarar da suka gabata, mata ne suka cika gurabe da dama na wuren aiki a karo na farko, binciken gwamnati ne ya nuna hakan.

Suna cikin mazauna Saudi da a yanzu ake gani suna sallamar kwastomomi a wuraren saida abinci, shaguna, shagunan saida takalma, waruren saida man fetur, wanda a da bakin haure ne ke yi.

A al'adance, an haramtawa matan Saudi cudanya da maza a wurin da ba danginsu.

Insaf, mahaifar yara uku mai shekaru 30 ta ce, ta zama direba ne bayan rasuwar mijin ta kwanan nan.

"Bai bar mana dukiya ba, saboda haka ya zama min dole in yi aiki don tallafawa yara na," ta bayyana wa AFP, inda ta zaba amfani da wani suna daban saboda tsaro.
"Ina amfani da motar marigayin mijina wajen daukar mata da yara a makwabtan don kai su makarantu ko kasuwanni.
"Aiki a matsayin direba ya bani sabuwar dama a rayuwa".

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Wata Kasar Turai Ta Dakatar Da Dokar Wajabta Yin Riga Kafin Korona

Tun a shekarar 2018, sama da mata 200,000 sun samu lasisin tuki, da dagawar farashin mota 5% a shekarar da ta gabata, kamar yadda yanar gizo ta ruwaito.

Wata fasinja Aya Diab, mai shekaru 29 ta bayyana yadda tafi samun walwala a ma'amalar ta da matan. Sannan wata kwastoma 'yar kasar Saudi, wacce ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana ra'ayi mai kama da hakan.

"Ji nake kamar ina tare da yar uwata," a cewarta, yayin zama a kujerar gaba kusa da Fahd.

Asali: Legit.ng

Online view pixel