Ku barmu mu tara gashi: Shehu Sani ya kai ziyara ofishin Hisbah, ya mika bukatarsa

Ku barmu mu tara gashi: Shehu Sani ya kai ziyara ofishin Hisbah, ya mika bukatarsa

  • Sanata Shehu Sani ya kai ziyara ofishin hukumar Hisbah ta jihar Kano a ranar Litinin, 14 ga watan Maris
  • Sani wanda ya sha caccakar Hisbah a baya, ya ce ya ziyarce su ne domin ya gane wa idonsa al’amura, ya kuma shawarci hukumar da su kara fadada ayyukanta
  • Sanata Shehu Sani ya kuma roka cikin raha da cewa ‘yan Hisbah ya kamata su bar masu yin aski afro, kamar dai shi dinnan su tara suma

Kano - Dan siyasa kuma mai rajin kare hakkin dan Adam, Sanata Shehu Sani a ranar Litinin, 14 ga watan Maris ya ziyarci shahararriyar hukumar Hisbah ta jihar Kano.

Da yake zantawa da manema labarai kan ziyarar, Sanata Sani ya ce ya je ofishin hukumar ne domin neman bayani kan wasu abubuwa da kuma sanin ayyukan Hisbah biyo bayan cin karo da ya yi da labarai da dama da ake danganta su da hukumar a fadin jihar.

Kara karanta wannan

2023: Wani Farfesan Najeriya Ya Yunƙuro, Zai Nemi Kujerar Buhari a Ƙarkshin Jam'iyyar APC

Shehu Sani ya kai ziyara ofishin Hisbah
Ku bar mutane su yi aski Afro: Shehu Sani ya kai ziyara ofishin Hisbah, ya mika bukatarsa
Asali: Facebook

Jawabin Shehu Sani ga manema labarai

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa:

“An fadi abubuwa da yawa game da Hisbah kuma na yi imanin cewa a matsayina na tsohon Sanata, mai fafutukar kare hakkin bil’adama da na jama’a, a zahiri ya kamata in ziyarci ofishinsu na ji ta bakinsu inji wane irin aiki suke yi da nauyin da ya rataya a wuyansu da kuma batutuwan da ake danganta su da su.”
"Na yi farin ciki da jin cewa ba su hana wadanda suke da sha'awar ci gaba da tara suma kamar ni ba saboda na zo ne don kare 'yancin mutanen da ke son tara suma.
“Na biyu kuma, sun fada min a zahiri cewa suna adawa da samar da, sarrafa, sayarwa, sha, da kuma mallakar barasa mai sa maye a jihar.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa a yaki

“Sun ce mani suna da ka’idar sanya suturar da idan ka keta doka, za ka fuskanci fushin doka. Batun mutun-mutumin sayar da kaya, ba zai yiwu a ajiye su da kai ba. Game da fina-finai da wasannin kwaikwayo. Yana da kyau a yi hulda da wata cibiya kamar tasu.
“A matsayinsu na ‘yan sandan addini, ya zama wajibi su hada kai su ga yadda za su yaki ‘yan fashi da ta’addanci a Najeriya.
“’Yan ta’adda na amfani da sunan Musulunci wajen lalata sunan Musulunci da Musulmi.
“Bukatar hukumar Hisbah ta shirya kanta tare da tunkarar ‘yan ta’adda da ‘yan fashi a akidance yana da matukar muhimmanci. Da bukatar su shiga tsakani wajen zaburar da jama’a domin yakar ‘yan fashi da ta’addanci a yankin Arewacin Najeriya.
“Har ila yau, akwai bukatar su tuntubi al’ummomin karkara tare da wayar da kan ‘yan kasar mu kan kada su shiga cikin ‘yan bindiga kuma yakar ta’addanci ma na da matukar muhimmanci.

Kara karanta wannan

Wani dan jarida: Irin azabar dana sha a hannun Abba Kyari bisa umarnin wani gwamna

"Don haka, baya ga aiwatar da dokar addini, akwai bukatar wannan gabar su kasance cikin shiri, da himma, da kuma jajircewa wajen neman mafita mai dorewa kan matsalolin rashin tsaro da ke addabar mutanenmu."

Sanata Sani ya kuma bayyana bidiyon ziyarar tasa ta shafinsa na Twitter.

Kaduna: Baya ga hari a masallaci, 'yan bindiga sun hallaka mutane, sun sace wasu mata

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kan titin Fumigi da ke Unguwan Galadima, Gonin-Gora, cikin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, sun kashe mazauna tare da sace wasu mata biyu.

Mataimakin shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Arewa, Rabaran John Hayab ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne kwanaki uku da sace wani limamin cocin Katolika, Rabaran Joseph Akete na cocin St. John Catholic, Kudenda da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel