Bayan Cikar Wa'adin Yajin Aikin Gargadi, ASUU Za Ta Yi Taro a Yau

Bayan Cikar Wa'adin Yajin Aikin Gargadi, ASUU Za Ta Yi Taro a Yau

  • A yayin da wa'adin sati hudu da kungiyar ASUU ta bayar na yin yajin aikin gargadi ke cika, kungiyar za ta yi taro a yau Lahadi.
  • Wani daga cikin shugbannin kungiyar ya bayyana cewa akwai alamun za a cigaba da yajin aikin domin babu wani cigaba da aka samu kawo yanzu
  • Kungiyar ta ASUU ta tafi yajin aikin ne saboda rashin cika mata alkawurra da ke cikin yarjejeniyar da ta yi da gwamnatin tarayya da suka hada da batun IPPIS, rashin biyan alawus da sauransu

FCT, Abuja - Kwamitin shugabannin kungiyar malaman jami'o'in Najeriya, ASUU, za ta yi taro a yau Lahadi, The Punch ta rahoto.

Za a yi taron ne a babban birnin tarayya Abuja domin yin nazari kan yajin aikin da kungiyar ke yi, a cewa wani mamba a kwamitin shugabannin.

Kara karanta wannan

Abba Kyari ya sake shiga 3, kwamitin binciken EndSARS na bukatar NDLEA ta mika shi

Bayan Cikar Wa'adin Yajin Aikin Gargadi, ASUU Za Ta Yi Taro a Yau
ASUU Za Ta Yi Taro a Yau, Akwai Yiwuwar Cigaba Da Yajin Aikin. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Eh, za mu yi taro yau kan yajin aikin da muke yi da wasu batutuwa."

Da aka masa tambaya ko za su janye yajin aikin bayan taron, ya bada amsa da cewa:

"Da wuya hakan ta yiwu. Babu wata cigaba na alheri da na sani."

Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, shima ya tabbatar da taron amma bai yi karin bayani ba.

Taron ne zuwa ne kwana daya bayan cikar wa'adin yajin aikin gargadi da ASUUn ta yi.

Ainihin dalilinnda yasa ASUU ta tafi yajin aikin

Kungiyar, a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairun 2022, ta tafi yajin aiki na gargadi na makonni 4.

A cewar kungiyar, ta tafi yajin aikin ne saboda kin cika mata alkawurra da ke cikin yarjejeniyarta da gwamnatin tarayya da aka rattaba hannu kansa a 2009.

Kara karanta wannan

A kan bashin N2.7m da ta ke bin sa, magidanci ya nada wa matarsa mai juna biyu dukan mutuwa

ASUU ta kumma zargi Gwamnatin Tarayya da yin zagon kasa ga amincewa da tsarin biyan albashi na UTAS, wacce ASUU ta kirkira a madadin IPPIS.

A hirar da aka yi da shi a Channels Television a ranar Asabar, Osadeke ya ce:

"Babu wani abin azo a gani da aka yi kawo yanzu. Mun yi taro da Ministan Kwadago sau biyu.
"Mun bawa NIREC daman ta shiga tsakani kuma ta yi. Abin da muke gani shine rashin damuwa da jami'un gwamnati.
"Bai kamata yajin aikin ya wuce sati daya ba idan da gwamnati ta dauki abin da muhimmanci, Da suka samu matsala da Ukraine inda yayan masu kudi ke karatu, mun ga yadda suka fitar da kudi cikin gaggawa, amma a kasa inda yayan talakawa ke karatu, ba a yi komai ba."

Gwamnatin Tarayya ta dage cewa UTAS ba ta ci gwaje-gwajen da aka yi ba domin fara amfani da shi a matsayin tsarin biyan albashin malaman jami'a.

Kara karanta wannan

Daga rubutu a Twitter: An daure 'yar jarida saboda yiwa shugaban kasa gugar zana

Ra'ayin wani malami a jami'ar tarayyar Najeriya dangane da yiwuwar cigaba da yajin aikin ASUU

Legit.ng Hausa ta tuntubi wani malami daga daya cikin manyan jami'ar tarayya don jin ra'ayinsa kan yiwuwar cigaban yajin aikin.

Malamin da ya bukaci kada a ambaci sunansa ya ce shi yana goyon baya a cigaba da yajin aikin domin rashin adalci ne gwamnati ke yi wa malamai kan rashin cika musu alkawurra da ke cikin yarjejeniyar da aka rattaba hannu kai.

Malamin ya ce:

"Ni ina ganin a cigaba da yajin aikin har sai gwamnati ta cika wa ASUU alkawurran da ke cikin yarjejeniyarsu domin babu amfani a janye yakin aikin, bayan kwana biyu a sake komawa. Gara kawai a yi ta ta kare.
"Babu yadda malamai za su iya yin aikinsu yadda ya dace idan ba su samun hakokinsu da suka shafi allawus, ariyas da sauran abubuwan da ake bukata wurin koyar da dalibai."

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar da ya rika karbar albashin N15, 000 ya rasu

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel