Daga rubutu a Twitter: An daure 'yar jarida saboda yiwa shugaban kasa gugar zana

Daga rubutu a Twitter: An daure 'yar jarida saboda yiwa shugaban kasa gugar zana

  • Wata 'yar jarida ta sha daurin shekaru biyu da watanni yayin da aka kama ta da laifin zagin shugaban kasa
  • Rahotanni sun bayyana cewa, an kama ta laifin yin gugar zana kan mulkin shugaban Turkiyya Erdogan
  • A bangare guda, 'yar jaridar ta bayyana cewa, ba da shugaban kasa take ba, amma dai tana 'yancin sukar gwamnati

Turkiyya - An yankewa wata fitaccen 'yar jaridan kasar Turkiyya hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari saboda samunta da laifin yin gugar zana da ake zargin ta yi sa ne game da fadar shugaba Erdogan da shi kansa.

An dauki wannan sukan nata a matsayin gugar zana ga shugaba Recep Tayyip Erdogan game da zamansa a kujerar mulki ta alfarma.

Wata ta zagi shugaban kasa, za ta zauna a gidan kaso
Zagin manya: Dan Jarida zai yi zaman kaso saboda rugawa shugaban kasa ashariya | Hoto: tmgrup.com.tr
Asali: UGC

An ce wata kotun Istanbul ta samu Sedef Kabas da laifin cin mutuncin shugaban kasa tare da yanke mata hukuncin daurin shekaru biyu da watanni hudu, kamar yadda kungiyar lauyoyin MLSA ta sanar a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Yin arziki 'yan Crypto zai tabbata: Amurka ta juyo kan 'yan Crypto, za su ga canji nan kusa

Bayan yanke hukuncin, an saki Kabas daga tsarewar da aka yi mata na wucin gadi, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

A cikin watan Janairu, 'yar jaridar ta yi Allah-wadai da wasu abubuwan da suka shafi mugunyar hanyar da gwamnatin Turkiyya ke yi wa masu sukarta a wani shirin talabijin.

Bayan haka kuma a shafinta na Twitter, ta yi wata magana mai kama da gugar zana ga shugaban kasar na Turkiyya da kuma fadarsa.

Ba ta fito karara ta ambaci sunan Erdogan ko fadarsa ta Ankara ba.

A cewar kungiyar lauyoyin, Kabas ta fada a zauren kotun cewa ba ta zagi shugaban kasa ba, amma tana da 'yancin ta soki gwamnati, hakan kuma shi ne aikinta a matsayin 'yar jarida, kamar yadda People Gazette ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce

Yakin Ukraine da Rasha: Burtaniya ta daskarar da kadarorin mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea

A wani labarin, kasar Burtaniya ta daskarar da kadarorin mai kungiyar kwallaon kafa ta Chelsea Roman Abramovich, kana ta sanya haramcin mu'amala da daidaikun mutane da 'yan kasuwa na Burtaniya, da dokar hana zirga-zirga duk dai akansa.

Sky Sports ta rahoto Firayim Ministan Burtaniya, Boris Johnson yana cewa:

"Ba zai yiwu a samar da mafaka ga wadanda suka goyi bayan mummunan harin da Putin ya kai wa Ukraine ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel