Neja: 'Yan Ta'adda Sun Farmaki Kasuwa, Sun Yi Kisa, Sun Sace Mutane Da Kayan Abinci Masu Yawa

Neja: 'Yan Ta'adda Sun Farmaki Kasuwa, Sun Yi Kisa, Sun Sace Mutane Da Kayan Abinci Masu Yawa

  • Wasu miyagun yan ta'adda sun kai hari kasuwar kauyen Chibani a karamar hukumar Munya, Jihar Neja a ranar Juma'a
  • Yayin harin sun halaka dan kasuwa daya sun kuma sace mutane da dama da kayan abinci tare da lalata wasu kayayakin
  • Wani dan garin ya ce maharan sun afka musu ne misalin karfe 12 na rana lokacin kasuwan na cike makil suka shafe kimanin awa uku suna cin karensu ba babbaka

Neja - A kashe a kalla dan kasuwa guda daya an kuma sace wasu da ba a san adadinsu ba yayin da masu garkuwa da mutane suka kai hari wani kasuwar kauye a Chibani, karamar hukumar Munya, Jihar Neja.

Daily Trust ta rahoto cewa yan ta'addan sun kuma kai hari garin Mararaban-Daudu, shima a karamar hukumar Munya, suka sace mutane duk a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Kaduna: Bayan karbe kudin fansa, 'yan bindiga sun sheke wanda suka sace

Neja: 'Yan Ta'adda Sun Farmaki Kasuwa, Sun Yi Kisa, Sun Sace Mutane Da Kayan Abinci Masu Yawa
Neja: 'Yan Ta'adda Sun Afka Kasuwa, Sunyi Kisa Sun Sace Mutane Da Kayan Abinci. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Mazaunin garin Munya ya tabbatar da harin

Shehu Abubakar, wani mazaunin garin ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa maharan sun afka garin ne misalin karfe 12 na rana lokacin kasuwan na cike makil suka shafe kimanin awa uku suna cin karensu ba babbaka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Trust Saturday ta tattaro bayanai cewa yan ta'addan sun sace kayayyakin abinci bayan yan kasuwan sun tsere.

"Ba mu san inda yan kasuwa da dama suke ba a yanzu saboda ba su fara dawowa ba. An lalata kayayyakin masarufi da dama bayan wadanda suka sace.
"Har zuwa karfe 5 na yamma, yan kasuwan ba su koma kasuwa sun kwashe kayansu ba. An kashe mutum daya, an kai gawarsa ofishin yan sanda ta Sarkin Pawa," in ji shi.

Da aka tuntube shi, mai magana da yawun yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ya ce a dakace shi ya yi bincike kuma bai bada bayani ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Yin arziki 'yan Crypto zai tabbata: Amurka ta juyo kan 'yan Crypto, za su ga canji nan kusa

A yan kwana-kwanan nan, yan ta'adda suna yawan fasa shagunan mutane suna sace abinci daga kauyuka a Jihar Niger.

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel