Kaduna: Bayan karbe kudin fansa, 'yan bindiga sun sheke wanda suka sace

Kaduna: Bayan karbe kudin fansa, 'yan bindiga sun sheke wanda suka sace

  • 'Yan bindiga sun halaka wani bawan Allah da suka sace bayan sun karbe kudin fansa
  • Labarin mutuwar ya zo ne a daren Talata bayan yan uwan marigayin sun kai ma yan bindigar naira miliyan daya da suka bukata
  • Har yanzu akwai sauran mutanen da aka sace su tare a hannun yan bindigar ciki harda wata mai shirin zama amarya

Kaduna - Yan bindiga sun kashe wani mutum da suka sace bayan sun karbi naira miliyan daya a matsayin kudin fansa daga yan uwansa, Daily Trust ta rahoto.

A watan Fabrairu ne yan bindiga suka farmaki gidan mutumin a yankin Rigachikun da ke karamar hukumar Igabi sannan suka sace shi da wasu a yankin ciki harda mai shirin zama amarya.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a Kaduna, rayuka sun salwanta

Kaduna: Bayan karbe kudin fansa, 'yan bindiga sun sheke wanda suka sace
Kaduna: Bayan karbe kudin fansa, 'yan bindiga sun sheke wanda suka sace Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A yayin mamayar, an harbe wani jami’in kwastam da ke aiki da FOU Zone B, Kaduna sannan daga bisani ya mutu a asibiti.

Wata mata a yankin ta fada ma Daily Trust cewa labarin mutuwar mutumin ya zo ne a daren Talata bayan yan uwan marigayin sun kai ma yan bindigar kudin fansa.

Ta ce:

“Sun harbe shi bayan sun karbi kudin fansa daga mutumin da ya kai masu kudin. Dukkanin mazauna yankin na cikin alhini bayan sun sami labarin mutuwar."

An tattaro cewa an yi jana’izar mutumin a garin Unguwar Shanu inda iyalansa ke da zama.

Dailypost ta kuma rahoto cewa har yanzu amaryar da wani mutum daya suna a hannun wadanda suka yi garkuwa da su din.

Yan bindiga sun yi garkuwa da Amarya ana gab da aurenta da wasu mutum 5 a Kaduna

Kara karanta wannan

Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce

A baya mun ji cewa yan bindiga sun farmaki Anguwar Rigachikun, dake karamar hukumar Igabi, cikin garin Kaduna, sun sace wata budurwa dake shirin zama amarya da wasu mutum 5.

Daily Trust ta tattaro cewa yan ta'addan sun kai hari yankin wanda ke kusa da Kasan Dam da misalin karfe 1:00 na daren ranar Laraba.

Maharan sun kutsa gida bayan gida suka zabi wasu mutane dake zaune a yankin, cikinsu harda Amarya mai shirin fara Amarci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel