Ramadan: Sarkin Kano Ya Yi Kira Ga Ƴan Kasuwa Kada Su Ƙara Farashin Kayan Abinci

Ramadan: Sarkin Kano Ya Yi Kira Ga Ƴan Kasuwa Kada Su Ƙara Farashin Kayan Abinci

  • Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga yan kasuwan Kano su guji kara farashin kayan abinci gabanin zuwa azumin watan Ramadan
  • Sarkin ya yi wannan kirar ne yayin wata addu'a ta musamman da aka yi a babban masallacin Kano don murnar cikarsa shekaru biyu a kan karagar mulkin Kano
  • Sarki Aminu Ado Bayero ya ce idan har suna neman albarka daga Allah to ya kamata su kasance masu saukaka wa al'umma yan uwansu musamman a watan Ramadan

Jihar Kano - Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi kira ga yan kasuwa a jiharsa su guji kara kudin kayan abinci a jihar a yayin da azumin watan Ramadana ke karatowa.

Daily Trust ta rahoto Sarkin ya yi wannan kirar ne yayin wata addu'a ta musamman da aka yi don murnar cikarsa shekaru biyu a kan karagar mulkin Kano.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya bayar da gudunmawar miliyan N30 ga iyalan yan-sa-kai da aka kashe a Kebbi

Ramadan: Sarkin Kano Ya Yi Kira Ga Ƴan Kasuwa Kada Su Ƙara Farashin Kayan Abinci
Ramadan: Sarkin Kano Ya Shawarci Ƴan Kasuwa Kada Su Ƙara Farashin Kayan Abinci. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarkin, wanda ya mika godiya ga Allah saboda yi masa jagora da bashi damar yi wa mutanensa hidima, ya bukaci su guji kara kudin kayan abinci don samun albarkacin watan ramadan.

Sarki Aminu Ado Bayero ya yi godiya ga masarautar Kano, gwamnati da al'umma

Ya kuma mika godiyarsa bisa goyon baya da ya ke samu daga mambobin masarautar Kano da gwamnatin jihar da al'umma cikin shekaru biyun da suka shude, rahoton Daily Trust.

An yi addu'ar ta musamman ne a babban masallacin Kano, karkashin jagorancin babban limamin Kano, Farfesa Muhammad Sani Zaharadeen da Wazirin Kano, Alhaji Sa'ad Shehu Gidado.

Ramadan: Yadda Jarumin Kannywood, Naburaska Ya Tallafa Wurin Sakin Ƴan Gidan Yari 33

A wani labarin, Fitaccen jarumin fina-finan ban dariya na Kannywood, Mustapha Badamasi wanda aka fi sani da Naburaska a masana’antar fim, ya taimaka wurin sakin ‘yan gidan yari 33 a Kano.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya bada umurnin cire Buni, ya so ya ha'ince mu: El-Rufai

Ya samu nasarar sakin maza 31 da mata biyu a gidan gyaran halin Goron Dutse da ke Jihar Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Jarumin ya bayyana dalilin sa na yin hakan inda yace yana so ya faranta wa mutane rai ne musamman ganin yadda watan Ramadan yake kara matsowa kuma ya hori sauran mutane da su bi sahun sa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel