Shugaba Buhari ya bada umurnin cire Buni, ya so ya ha'ince mu: El-Rufai

Shugaba Buhari ya bada umurnin cire Buni, ya so ya ha'ince mu: El-Rufai

  • Gwamnan jihar Kaduna ya fasa kwai kan rikicin da ya barke cikin jam'iyya mai ci All Progressives Congress (APC)
  • El-Rufa'i a hirar da yayi yace Mai Mala Buni ya yi kokarin cigaba da zama kan kujerar shugaban jam'iyya
  • A cewarsa gwamnoni 19 yanzu haka na goyon bayan sabon shugaban jam'iyya kuma gwamnan Neja

Abuja - Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ba zai taba komawa kujerar Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana hakan.

A hirar da yayi a shirin Politics Today, El-Rufa'i ya ce Buni ko ya dawo an fitittikeshi daga kujerar gaba daya har abada.

Mai Mala Buni
Shugaba Buhari ya bada umurnin cire Buni, ya so ya ha'ince mu: El-Rufai Hoto: Mai Mala Buni
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ba rikicin APC ya damu talaka ba, yan jarida na batawa kansu lokaci kan rikicin APC, Buhari

Ya ce Shugaba Buhari da gwamnonin APC 19 sun yi ittifaki kan cire Mai Mala Buni.

El-Rufa'i yace:

"Buni ya tafi har abada, Sakatare ya tafi. Gwamna Bello ne kan kan kujerar yanzu kuma Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnoni 19 na bayansa. Buni ko ya dawo zai dawo ne a matsayin Gwamnan Yobe amma ba Shugaban jam'iyyarmu ba."
"Shugaba Buhari ya bada umurnin cireshi. Buni da mutanensa sun samu wata doka daga kotu na hana taron gangami amma ya boye."
"Ban san dalilin da zai sa mutum yayi irin haka ba."

Kalli bidiyon:

Gwamna Mai Mala Buni ya baiwa Buhari hakuri, yace a bari ya dawo kujerarsa

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya roki Shugaba Muhammadu Buhari ya bari ya dawo kujerarsa zuwa bayan taron gangamin APC da za'ayi nan da makonni biyu.

A bisa rahoton Thisday, Buni ya tuntubi Shugaba Buhari ya gafarta masa bisa tuhume-tuhumen da ake masa kuma a bari ya dawo kujerarsa saboda kada rikici ya barke a jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta yi amai ta lashe, tace har yanzu Gwamna Mala Buni ne shugabanta

Bugu da kari, wasu gwamnoni masu goyon bayan Mal Mala Buni sun roki Buhari ya bari Buni ya kammala aikinsa matsayin Shugaban APC, ya mika mulki ga sabbin shugabanni sannan ya sauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel