Ramadan: Yadda Jarumin Kannywood, Naburaska Ya Tallafa Wurin Sakin Ƴan Gidan Yari 33

Ramadan: Yadda Jarumin Kannywood, Naburaska Ya Tallafa Wurin Sakin Ƴan Gidan Yari 33

  • Fitaccen jarumin Kannywood, Mustapha Badamasi wanda aka fi sani da Naburaska ya taimaka wurin gaggauta sakin wasu ‘yan gidan yari 33 a Kano
  • Cikin wadanda yasa aka saki akwai maza 31 da mata 2, kuma yace babban dalilin sa shi ne faranta wa mutane da dama rai musamman ganin watan Ramadan yana kusa
  • Ya bukaci sauran mutane masu mukamai daban-daban da kuma dukiya da su tallafa wa rayuwar mazauna gidan yarin musamman wadanda ake bin su tarar da suka kasa biya

Kano - Fitaccen jarumin fina-finan ban dariya na Kannywood, Mustapha Badamasi wanda aka fi sani da Naburaska a masana’antar fim, ya taimaka wurin sakin ‘yan gidan yari 33 wadanda ke zama a gidan gyaran halin Goron Dutse da ke Jihar Kano.

Kara karanta wannan

Mu ne muka kashe kasar nan, ya kamata yanzu ina gidan kurkuku inji Tsohon Ambasada

Ya samu nasarar sakin maza 31 da mata biyu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ramadan: Yadda Jarumin Kannywood, Naburaska Ya Tallafa Wurin Sakin Ƴan Gidan Yari 33
Ramadan: Jarumin Kannywood, Naburaska Ya Tallafa Wurin Sakin Ƴan Gidan Yari 33. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Jarumin ya bayyana dalilin sa na yin hakan inda yace yana so ya faranta wa mutane rai ne musamman ganin yadda watan Ramadan yake kara matsowa kuma ya hori sauran mutane da su bi sahun sa.

Sun nuna jin dadin su akan taimakon da jarumin ya yi musu

Daily Trust ta ruwaito yadda ya ce, ya yi hakan ne da niyya mai kyau tare da neman lada daga Ubangiji, inda ya ce:

“Babu dadi mutum ya yi azumi a cikin gidan gyaran hali, hakan yasa na ga muhimmancin biyan kudi don a saki wasu daga cikin su.”

Ya bukaci masu hannu da shuni da kuma kamfanoni da su kwaikwayi irin abinda ya yi don su tallafa wa rayuwar mutanen da ke zama a gidan yari saboda kasa biyan bashin da ake bin su.

Kara karanta wannan

Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Yi Ƙarin Haske Kan Jitar-Jitar Cewa Ya Shiga Hannun Ƴan Bindiga

Yayin jawabi a maimakon ‘yan gidan yarin da aka saki, Mado Bala ya yi wa jarumin godiya kuma ya yi alkawari za su kasance masu kyawawan dabi’u don sun sha bakar wahala a gidan.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Asali: Legit.ng

Online view pixel