Zai shilla Amurka: Yaron da ya kwaikwayi gadar sama ta Kano ya samu 'Scholarship'

Zai shilla Amurka: Yaron da ya kwaikwayi gadar sama ta Kano ya samu 'Scholarship'

  • Musa Sani, wani yaro dan Najeriya da ya gina wata gadar sama ta Kano, ya samu daukaka da dajara samu fikirarsa
  • Wannan ya faru ne yayin da wani kamfanin gine-gine ya ga kyakkyawan kirkirrar da yayi kuma ya ba shi gurbin karatu a kasar Amurka
  • An kuma baiwa dukkan danginsa kyautar wani abu na musamman inda mahaifiyarsa ta samu Naira miliyan daya kuata da kana aka ba mahaifinsa aiki

Hazakar wani yaro ta zama silar ingantuwar rayuwar iyalansa yayin da wani kamfanin gine-gine ya ga kyakkyawan aikinsa.

Yaron dan Najeriya mai suna Musa Sani ya ba mutane sha'awa a yanar gizo bayan da ya gina wani kwafin gadar sama ta jihar Kano da ya gina da tarkacen wasan yara.

Yaro zai shilla Amurka saboda ginin gada
Zai shilla a Amurka: Yaron da ya kwaikwayi gadar sama ta Kano ya samu 'Scholarship' | Hoto: Aminu Adamu Abdullahi
Asali: Facebook

Albarka ta zagaya da iyalansa

Wani dan Najeriya mai suna Aminu Adamu Abdullahi da yada hotunan Musa da kirkirarsa a Facebook, ya bayyana cewa wani kamfanin gine-gine mai suna Ronchss Global Resources, ya baiwa Musa tallafin gurbin karatu a jami’ar kasar Amurka.

Kara karanta wannan

Zan hadu da rabo na: Mai digirin da ke tallan 'yan kamfai ya ce bai fidda rai da yin arziki ba

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aminu ya kara da cewa, kamfanin gine-ginen ya kuma baiwa mahaifiyar Musa kyautar Naira miliyan daya domin ta fara kasuwanci, yayin da aka baiwa mahaifinsa aikin yi.

Sun kuma yi alkawarin sanya ’yan uwan Musa a makarantu masu kyau sannan kuma za su kaurar da iyalan su Musa zuwa wani makeken gida a Maiduguri.

Mutane suna murna da ci gaban da iyalan su Musa suka samu

Nuruddeen Ibrahim Kafinta ya ce:

"MashaAllah. Wannan kyauta ce da albarka daga Allah."

Centina J Aridi ya ce:

"Ina taya ku murna da jin haka..Na yi farin ciki da jin wannan. Eunice

Alonge Obaro ya ce:

"A banza, tabbas ubansa zai auri mata da yawa ya kara haihuwa."

Sabiu Ibrahim yace:

"Wannan abin a yaba ne. Ya kamata mu sanya wannan hoto ko bidiyo ya yadu ya zagaya yanar gizo da sauri don karfafa yara da Ronchess Global Resources."

Kara karanta wannan

Ta Kacame: Mai Garkuwa Ya Yi Ƙorafi a Kotu, Ya Ce Abokansa Sun Cuce Shi Sun Bashi N200,000 Kacal Cikin N12m Da Suka Samu

Zan hadu da rabo na: Mai digirin da ke tallan 'yan kamfai ya ce bai fidda rai da yin arziki ba

A wani labarin, wani matashi, Charles Ifeco, mai sayar da ’yan kamfai a baro ya yada wani bidiyonsa mai ban sha’awa a yanar gizo yayin da ya zaburar da mutane kan a kama sana'a.

A cikin gajeren faifan bidiyon, matashin ya nuna irin kokarinsa na neman kudi, inda ya nuna kalan kayan da yake sayarwa ba tare da nuna kin sana'ar ba, kana yake fatan samun canji.

A faifan bidiyo da aka yada a shafin Instagram, Charles ya shiga gaban kamera, yana tambayar mutane ko suna jira su ga yadda rayuwa za ta sauya masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel