Zan hadu da rabo na: Mai digirin da ke tallan 'yan kamfai ya ce bai fidda rai da yin arziki ba

Zan hadu da rabo na: Mai digirin da ke tallan 'yan kamfai ya ce bai fidda rai da yin arziki ba

  • Wani matashi ya nuna bajintarsa ta hanyar da ba a saba gani ba yayin da ya hada bidiyo na hotunan kasuwancinsa da sauyin da yake samu
  • A bidiyon an ga matashin mai siyar da kayan sawa a baronsa yana sanye da kayan 'yan bautar kasa; NYSC
  • Jama’a da dama da suka ga bidiyon nasa sun yi masa addu’a, sun ce wata rana fafutukarsa za ta haifar masa da mai ido

Wani matashi, Charles Ifeco, mai sayar da ’yan kamfai a baro ya yada wani bidiyonsa mai ban sha’awa a yanar gizo yayin da ya zaburar da mutane kan a kama sana'a.

A cikin gajeren faifan bidiyon, matashin ya nuna irin kokarinsa na neman kudi, inda ya nuna kalan kayan da yake sayarwa ba tare da nuna kin sana'ar ba, kana yake fatan samun canji.

Kara karanta wannan

Maryam Booth: Na gaji da amsa tambayar yaushe zanyi aure da me yasa na rame

Matashi mai tallan 'yan kamfai
Zan hadu da rabo na: Mai digirin da ke tallata a baro bai fidda rai ba, ya ce arziki nufin Allah ne | Hoto: @charlesifesco
Asali: Instagram

Allah zai yi min komai

A faifan bidiyo da aka yada a shafin Instagram, Charles ya shiga gaban kamera, yana tambayar mutane ko suna jira su ga yadda rayuwa za ta sauya masa.

Saurayin ya ci gaba da gaya wa mutane cewa har yanzu yana nan yana ci gaba da fafutuka kuma yana fatan watarana zai samu sauyin rayuwa.

Matashin ya ce ya san cewa kamar yadda Allah ya yi alkawari zai ba bayinsa karshen da ake tsammani mai kyau, shi ma zai yi nasara watarana.

Kalli bidiyon:

Martanin 'yan soshiyal midiya

A lokacin rubuta wannan rahoto, mutane sama 400,000 sun kalli bidiyon, tare da sharhi sama da 3,000.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin da mutane ke yi:

obaksolo ya ce:

Kara karanta wannan

Bidiyon jaruma Umma Shehu tare da diyarta yayin da suke girgijewa ya haifar da cece-kuce

"Wannan canjin yana nan kusa fiye da tunanin ka dan uwa, Insha Allah."

deyemitheactor ya ce:

"Wata rana ni kaina zan yi bidiyon canji lokacin da na daga!"

mama_adannaya yace:

"Abubuwan da muke tsammani ba za su gushe ba, muna sa ran za ka mana bidiyon canji da hotonka na canji. Allah ya dafa maka. Amin."

adeosho1 ya ce:

"Dan uwa na, tare zamu isa can da yardar Allah."

mentorc_1 ya ce:

"Allah ya jikan ka da rahama, duk za mu isa can wata rana kar ka karaya."

Rabo a kan rabo: Baiwar Allah ta haifi yara biyu a lokaci daya, kuma ba tagawaye ba ne

A wnai labarin, wata mata ta bada labarin yadda ta dauki ciki a lokacin da ta ke dauke da wani juna biyun. Kwanaki biyar ne tsakanin daukar cikin ‘ya ‘yan na ta.

Wannan labari mai ban mamaki ya zo a jaridar Daily Mail. Odalis Martinez ta bayyana yadda dadi ya kusa kashe ta bayan ta gano tana da ciki a karshen 2020.

Kara karanta wannan

Aure ya yi albarka: Hotunan magidancin da ya auri mata 2 a rana guda yayin da suke murnar cika shekara 1

A cewar Odalis Martinez, ta samu juna-biyun ne ‘yan watanni kadan bayan ta yi bari. A lokacin da ta je yin awo, sai ta gano ashe ‘ya ‘ya har biyu ma za ta haifa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel