El-Rufai ya fusata ABU Zaria, ASUU ta bukaci a soke Digirorin da aka ba shi a 1980

El-Rufai ya fusata ABU Zaria, ASUU ta bukaci a soke Digirorin da aka ba shi a 1980

  • ASUU ta yi zama a kan filin ABU Zaria da Nasir El-Rufai yake neman karbewa da karfi da yaji a Kaduna
  • Kungiyar ta bukaci hukumar makarantar ta karbe digirorin da aka ba Gwamnan na jihar Kaduna
  • El-Rufai ya samu shaidar B. Sc da MBA duk daga jami'ar ABU Zaria kusan shekaru 40 da suka wuce

Kaduna - Kungiyar malaman jami’a na reshen jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta yi kira ga shugabannin jami’ar da su karbe digirorin Nasir El-Rufai.

Rahoto ya fito daga jaridar Abusites cewa kungiyar ASUU ta cin ma matsaya cewa a raba Malam Nasir El-Rufai da shaidar karatun da ya samu a jami’ar.

Hakan na zuwa ne bayan sabanin da aka samu tsakanin mai girma gwamnan na jihar Kaduna da shugabannin jami’ar ABU Zaria game da batun wani fili.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Kungiyar ta ce abubuwan da gwamnan na Kaduna yake yi, sun ci karo da koyarwa da tarbiyar da ya samu daga wannan babbar jami’a mai dadadden tarihi.

ASUU ta cin ma wannan mataki bayan zaman da tayi a Samaru Zaria a ranar Laraba, 2 ga watan Maris 2022, a karkashin jagorancin Farfesa Haruna Jibril.

Sabon shugaban ASUU da sakatarensa a ABU Zaria, Haruna Jibril da Husseini Abdullahi su ka sa hannu a takardar da aka fitar bayan wannan zaman a jiya.

El-Rufai
Gwamna Nasir El-Rufai a bikin KASU Hoto: www.kasu.edu.ng
Asali: UGC

Takardar tana cewa malaman jami’ar sun tattauna a kan batun yunkurin gwamna Nasir El-Rufai na karbe filin ABU da karfi da yaji, duk da kotu ta hana shi.

Jawabin bayan taron ASUU

“ASUU-ABU Zaria a zamanta na 2 ga watan Maris 2022, ta zauna a kan yunkurin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai na karbe filin da ABU Zaria, cibiyar karatu ta gwamnatin tarayyar Najeriya, kuma tsohuwar jami’a mai tarihi ta mallaka.”

Kara karanta wannan

Duka Gwamnonin APC za su yi zaman musamman domin dinke sabuwar baraka kan mukamai

Rahoton ya ce ASUU ta tsaida magana cewa za ta je kwalejin aikin gona da gandun dabbobin da ke unguwar Mando ta shirya zanga-zanga domin nuna jin dadinta.

Sabon shugaban ASUU

Kwanan nan kungiyar ta ASUU ta shirya zaben shugabannin na ta na reshen jami’ar, inda Haruna Jibril wanda malami ne a sashen lissafi ya zama shugabanta.

Legit.ng Hausa ta fahimci an yi wannan zama ne a dakin taro na Abdullahi Smith da ke tsangayar fasaha. El-Rufai ya samu digiri biyu a jami’ar tun shekarun 1980s.

El-Rufai v ABU Zaria

Tun a watan jiya aka ji cewa Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zaria za ta sake shigar da karar Gwamnatin Nasir El-Rufai a kotu saboda zargin saba umarnin Alkali.

Duk da mai shari'a K. Dabo ya ce ka da kowa ya taba filin, sai aka ji jami'an KASUPDA sun yi watsi da umarnin kotu, sun fara ruguza filin DAC da ke Mando, garin Kaduna.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ’Yan Ta’adda Sun Kashe 7, Sun Sace 57, Sun Kuma Jikkata Dalibai Masu Zuwa Rubuta JAMB a Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel