Yan bindiga sun yi takansu yayin da jami'an tsaro suka far musu a jihar Katsina

Yan bindiga sun yi takansu yayin da jami'an tsaro suka far musu a jihar Katsina

  • Jami'an tsaro sun samu nasarar fatattakar yan bindiga da sukai yunkurin kai hari kauyen Barawa a jihar Katsina
  • Kakakin yan sanda na jihar, SP Gambo Isah, ya bayyana cewa dakarun yan sanda da Sojoji sun nuna wa yan ta'addan kwarewa da dabarun yaƙi
  • Hukumar yan sanda ta yi kira da mutanen jihar Katsina su cigaba da baiwa hukumomin tsaro haɗin kai

Katsina - Dakarun yan sanda sun dakile harin yan bindiga kuma suka kwato Babura 6 a ƙauyen Barawa dake ƙaramar hukumar Batagarawa, jihar Katsina.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Gambo Isa, shi ne ya shaida wa manema labarai haka ranar Talata a Katsina, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Yan bindiga a Katsina
Yan bindiga sun yi takansu yayin da jami'an tsaro suka far musu a jihar Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewarsa, Yan bijilanti ne suka fara ganin tawagar yan ta'addan da adadi mai hawa haye kan Babura kuma ɗauke da AK47 nan take suka sanar da yan sanda.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun bayyana gaskiyar abin da yasa Fulani Makiyaya suka halaka mutum 7 a Taraba

A kalamansa, SP Gambo Isa ya ce:

"Dakarun yan sanda da Sojoji suka shirya suka nufi yankin, suka yi musayar wuta da yan ta'addan kuma suka samu nasarar dakile yunkurin su."
"Dabarun yaƙi da jajircewar da dakarun tsaron Najeriya suka nuna ya sa tilas yan ta'addan suka bar kayan aikin su, suka yi ta kansu.Yayin binciken wurin gwabzawar suka gano Babura 6 na yan ta'adda suka ƙona su."
"Jami'ai sun sake gano wata Babur a jejin Barawa kuma mafi yawan yan bindigan sun gudu da raunin bindiga. Muna kira ga mutane su kawo mana rahoton duk wanda suka gani da raunin bindiga."

Rundunar yan sanda ta bukaci al'ummar jihar Katsina da kada su gajiya, su cigaba da ba su haɗin kai da sauran hukumomin tsaro a yaki da yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Yanzu: Bayan Shan Matsin Lamba Daga Mata, Majalisa Ta Canja Ra'ayinta Kan Dokar Mata, Za Ta Sake Sabon Kuri'a

A wani labarin kuma Uwar gida ta danna wa Mijinta wuka har lahira daga zuwa bankwana zai koma dakin Amarya

Tsagwaron kishin mata ya yi sanadin rasuwar wani Mai mata biyu yayin da yake yi wa Uwar gida bankwana zai koma dakin Amarya.

Rahoto ya nuna cewa Uwar gidan mai suna Atika ta daba wa mijinsu wuka har lahira a Mararaba dake jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel