Yadda aka yi ram da miyagun masu garkuwa da mutane a dajin Kwara

Yadda aka yi ram da miyagun masu garkuwa da mutane a dajin Kwara

  • 'Yan sintiri a jihar Kwara sun yi ram da wasu mutum goma wadanda ake zarginsu da addabar yankunan Obbo-Aiyegunle zuwa Ekiti
  • Kamar yadda kwamandan hukumar sintiri, Alhaji Saka Ibrahim ya sanar, an kama su ne a daji yayin da jami'ai suka kai samame
  • Ya sanar da cewa har yanzu mutanensu suna cikin daji kuma za su mika wadanda aka kama ga jami'an 'yan sanda

Kwara - Wasu mutum goma da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi yankin Obbo-Aiyegunle zuwa Ekiti a jihar Kwara sun shiga hannun hukuma.

An damke su ne bayan samamen da jami'ai suka kai wata maboyarsu da ke daji inda ake zargin suna adana wadanda suka sace, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe manoma 2 sannan sun yi garkuwa da wasu mutane 4 a Sokoto

Yadda aka yi ram da miyagun masu garkuwa da mutane a dajin Kwara
Yadda aka yi ram da miyagun masu garkuwa da mutane a dajin Kwara. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Yankin a cikin kwanakin nan ya shahara ta yadda masu garkuwa da mutane ke sace mutane kuma a kan samu gawawwakinsu bayan an biya kudin fansa.

Kwamandan hukumar sintiri ta jihar Kwara, Alhaji Saka Ibrahim, ya tabbatar da aukuwar lamarin ta wata tattaunawar waya da Daily Trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda yace:

"An damke wasu mutum bakwai a ranar Talata yayin da aka cafke wasu uku a ranar Laraba. Amma har yanzu jami'anmu na duba dajin. Za mu mika su hannun 'yan sanda idan sun fito daga dajin."

Bayan kalmashe N26m, 'yan ta'adda sun sako dagaci da wasu mutum 35 a Katsina

A wani labari na daban, Masu garkuwa da mutane sun sako dagaci da sauran mutane 35, bayan biyan N26 miliyan a matsayin kudin fansa, bayan wadanda aka yi garkuwan dasu sun kwashe kwana 29 a hannun 'yan bindigan kafin su sake su a yammacin Lahadi.

Kara karanta wannan

An kama wasu yan bindiga biyu, Fusatattun matasa sun kona su kurmus

'Yan bindiga sun sako dagacin Guga cikin karamar hukumar Bakorin jihar Katsina, Alhaji Umar da sauran mazauna kauyen guda 35 bayan amsar N26 miliyan a matsayin kudin fansa.

Premium Times ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka shiga kauyen a ranar 7 ga watan Fabrairu, inda suka halaka mazauna yankin guda 10 daga bisani suka yi awon gaba da mutane 36, duk da dagacin kauyen.

Babban da da sirikin basaraken ne suka tabbatar da sakin wadanda aka yi garkuwan dasu a daren Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel