Innalillahi: 'Yan bindiga sun yiwa diyar sarauta a Ibadan kisan gilla sun tsere

Innalillahi: 'Yan bindiga sun yiwa diyar sarauta a Ibadan kisan gilla sun tsere

  • An jefa birnin Ibadan cikin zaman makoki sakamakon kisan gillan da aka yi wa Fatimah, diyar tsohuwar Iyalode Aminat Abiodun da ta rage
  • An bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun harbe Fatimah ne a gidanta da ke unguwar Bashorun, Bodija a Ibadan a ranar Laraba, 9 ga watan Maris
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, ya ce nan ba da dadewa ba za a bayar da cikakken bayani kan kisan marigayiya Fatimah

Ibadan, Oyo - A ranar Laraba 9 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga suka harbe diyar tsohuwar Iyalode ta lardin Ibadan, marigayiya Alhaja Aminat Abiodun, wacce aka bayyana sunanta da Fatimah a gidanta dake unguwar Bashorun a birnin.

PM News ta ruwaito cewa ‘yan bindigan da suka kai farmaki gidanta da ke unguwar Bashorun, Bodija, Ibadan ne suka bindige Fatimah a ka.

Kara karanta wannan

An damke wanda ake zargi da kisan tsohon jami'in Soja da dogarinsa a Kaduna

An kashe diyar sarauta a jihar Oyo
Innalillahi: 'Yan bindiga sun yiwa diyar sarauta a Ibadan kisan gilla sun tsere | Hoto: @tolanialli
Asali: Twitter

An tattaro cewa ‘yan bindigan sun bar gidanta bayan sun tabbatar da cewa ta mutu kuma ba su dauki komai a gidan ba.

Wata majiyar dangi, wacce ta nemi a sakaya sunanta ne ta bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta bayyana cewa, an kai harin ne a gidanta ba tare da wani dalili ba, ganin cewa Fatima mai son zaman lafiya ce.

Majiyar ta kara da cewa:

“Bayanan da nake dasu, ‘yan bindigan sun harbe ta ne sau da yawa. Wannan babban rashi ne ga dangi."

An ruwaito Fatimah ita kadai ce diyar tsohuwar Iyalode da ta rage a duniya.

'Yan sanda sun magantu

Kamar yadda Daily Sun ta ruwaito, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, ya ce nan ba da jimawa ba za a bayar da cikakken bayani kan lamarin.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan sanda sun mutu yayin da motar tawagar ministocin Buhari ta yi hadari

Mahaifiyar Fatimah, tsohuwar mai rike da sarautar Iyalode, ta rasu ne a shekarar 2018 tana da shekaru 93. Ta wakilci mata a majalisar Olubadan daga 2007 zuwa 2018.

Karar kwana: Jami'an kwana-kwana sun ciro gawar matashiyar da ta nutse a rijiya a Kano

A wani labarin, rahotannin da muke samu sun bayyana yadda matashiya mai shekara 16; Hamida Bawale ta tsunduma kana ta nutse a cikin wata rijiya garin debo ruwa a kofar Fada Gidan Sarki a karamar hukumar Karaye a jihar Kano.

Wannan mummunan lamari na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Abdullahi ya fitar a ranar Talata 8 ga watan Maris a jihar Kano.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel