Karar kwana: Jami'an kwana-kwana sun ciro gawar matashiyar da ta nutse a rijiya a Kano

Karar kwana: Jami'an kwana-kwana sun ciro gawar matashiyar da ta nutse a rijiya a Kano

  • Wani mummunan yanayi ya faru a jihar Kano, inda wata matashiya ta fada rijiya ta nutse a karamar hukumar Karaye
  • Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta samu damar zuwa wurin da lamarin ya faru, inda aka yi gaggawan ciro ta
  • Rahoton da rundunar ta fitar ya bayyana yadda lamarin ya faru, kana ya ce an cire gawar matashiyar daga cikin rijiyar

Karaye, Kano - Rahotannin da muke samu sun bayyana yadda matashiya mai shekara 16; Hamida Bawale ta tsunduma kana ta nutse a cikin wata rijiya garin debo ruwa a kofar Fada Gidan Sarki a karamar hukumar Karaye a jihar Kano.

Wannan mummunan lamari na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Abdullahi ya fitar a ranar Talata 8 ga watan Maris a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Auran Sarauta: Sarkin Iwo zai angwance da jikar Sarkin Kano Ado Bayero, Firdausi

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

A cewarsa:

“Mun sami kiran gaggawa da misalin karfe 4:58 na yamma. daga ofishin yanki na civil defense na Karaye kuma muka aika da tawagarmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 5:04 na yamma.”

Ya kara da cewa an fito da Hamida daga cikin rijiyar amma aka samu ta mutu, kuma an mika gawar ta ga dan uwanta Abdullahi Bawale na Kofar Fada Gidan Sarkin Karaye.

Abdullahi ya ce, Hamida ta je debo ruwa a rijiyar ne aka sami akasi ta fada ciki.

Hakazalika, jaridar Vanguard ta kara da cewa, sanarwar ta kuma bayyana cewa marigayiyar tana da matsalar kwakwalwa.

Tsautsayi: Yadda jariri mai watanni 19 ya fada rijiya, ya nutse a jihar Kano

Kara karanta wannan

Karar kwana: Kasa ta rufta da mutum 5 a garin taya abokinsu hakar kasar ginin aurensa

A wani labarin, jaridar Daily Trust ta ruwaito faruwar wani mummunan lamari a jihar Kano ranar Talata yayin da wani jariri dan watanni 19 ya nutse a cikin rijiya da ke unguwar Al-Ansar da ke karamar hukumar Danbatta a jihar.

Lamarin da ya yi sanadin mutuwar jaririn ya faru ne a lokacin da mahaifiyarsa ta yi dan nisa da bakin rijiyar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar, Alhaji Saminu Abdullahi, ya ce sun samu kiran gaggawa daga wani Salisu Bello inda suka aika da tawagar agaji zuwa wurin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel