Wani hanin: Bayan shekaru 12 tana dako, Allah ya azurta mata da haihuwar 'ya'ya hudu nan take

Wani hanin: Bayan shekaru 12 tana dako, Allah ya azurta mata da haihuwar 'ya'ya hudu nan take

  • Bayan shafe tsawon shekaru 12 suna jiran tsamanni, Allah ya azurta wasu ma'aurata yan Najeriya da haihuwar 'yan hudu
  • Matar mai suna Onyinye Ezennia, ta je shafinta na sadarwa domin nuna godiya ga Ubangiji a kan wannan babban kyauta da ya yi mata
  • Ta wallafa kyawawan hotunansu tare da yaran wadanda suka zo a maza biyu, mata biyu

Lagos - Allah gwanin kyauta a duk lokacin da ya so ya azurta wasu ma’auratan Najeriya, Innocent da Onyinye Ezennia, da haihuwar ‘yan hudu bayan shekaru 12 da yin aure.

Sun yi taron godiya ga Allah wanda ya yi masu kyautan yaran, mata biyu da maza biyu cikin watan da ya gabata a cocin Assemblies of God, Ire-Akari Estate, Isolo, Lagos.

Wani hanin: Bayan shekaru 12 tana dako, Allah ya azurta mata da haihuwar 'ya'ya hudu nan take
Wani hanin: Bayan shekaru 12 tana dako, Allah ya azurta mata da haihuwar 'ya'ya hudu nan take Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

Misis Ezinnia ta wallafa hotunansu tare da yaran inda ta kwararo yabo ga Ubangiji kan wannan babban kyauta da ya yi mata bayan tsawon shekaru suna jiran tsammani.

Ta kuma yiwa sauran mata da ke neman haihuwa addu’a cewa da izinin Allah sune mutane na gaba da wannan abun al’ajabi zai riska.

Ga wallafar tata a kasa:

Wata mata mai shekaru 40 da ta haifawa mijinta 'ya'ya 44 tace ya gudu ya barsu

A wani labari na daban, mun ji cewa ba tare da samun wadataccen kulawar likita na musamman ba, wata mata mai suna Mama Uganda ta haifi yara 44 a tarayyarta da mijinta.

Matar da ta fito daga kasar Uganda ta fara haihuwa tun tana ‘yar shekara 13 bayan da iyayenta suka aurar da ita tana da shekara 12.

A cikin wani faifan bidiyo da wani mutum Joe Hattab ya yada a Facebook, matar mai shekaru 40 ta bayyana cewa ita uwa ce mara aure bayan mijinta ya yi watsi da su yayin da ya cika wandonsa da iska da kudadensu.

Matar a yanzu haka ita ke daukar dawainiyar yaranta har 38 gaba dayansu - 6 daga cikinsu sun mutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel