Hotunan tsoho mai shekaru 79 da yayi shekaru 30 a daji yana rayuwa shi daya

Hotunan tsoho mai shekaru 79 da yayi shekaru 30 a daji yana rayuwa shi daya

  • Mista Oh tsoho ne mai tsawon shekaru saba'in da tara a duniya kuma dan kasar Singapore wanda yayi tsawon shekaru shi kadai
  • Tsohon ya kwashe tsawon shekaru talatin a cikin wani daji da ke kusa da birnin Singapore amma babu wanda ya taba sanin inda yake
  • Yana rayuwarsa shi kadai tilo inda ya gina gidansa da katako tare da tamfal domin samun matsuguni da wurin kwana

Wani labari mai cike da al'ajabi shi ne na wani bawan Allah mai suna Oh dan asalin kasar Singapore.

Oh ya kwashe shekaru talatin na rayuwar sa yana zama a wani daji da ke kasar Singapore shi kadai tilo ba tare da kowa ba, The Nation ta ruwaito.

Ba zamansa bane a dajin babban abun mamakin, yadda babu wani mahaluki da ya taba gano inda Oh yake a cikin shekarun nan talatin ya zama babban abun al'ajabi.

Kara karanta wannan

Da ace EFCC na aikinta yadda ya kamata, da wasu masu neman kujerar Buhari suna kurkuku - Obasanjo

Tsohon mai shekaru saba'in da tara a duniya ya hada gidan da yake rayuwa a dajin ne da tamfal tare da itace a kusa da birnin Singapore.

Kamar yadda The Nation ta wallafa a shafinta na Twitter, ga hotunan tsohon a kasa:

Hotunan tsoho mai shekaru 79 da yayi shekaru 30 a daji yana rayuwa shi daya
Hotunan tsoho mai shekaru 79 da yayi shekaru 30 a daji yana rayuwa shi daya. Hoto daga @TheNationNews
Asali: Twitter

Ka fi Ronaldo: Bidiyon Obasanjo cike da kwarewa yana taka leda ya kayatar da 'yan Najeriya

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo ya shiga wasan kwallon kafan da aka yi a filin wasa na farfajiyar gidansa da ke Abeokuta a jihar Ogun.

Kamar yadda Channels TV ta ruwaito, wasan kwallon kafan yana daga cikin jerin shagulgulan cikan tsohon shugaban kasan shekaru tamanin da biyar.

Legit.ng ta tattaro cewa, a karamin wasan kwallon kafan, an ga shugaban kasar jamhuriyar Benin mai shekaru 91, Nicephore Soglo, tsohon ministan shari'a kuma antoni janar na tarayya, Bayo Ojo da sauran masoyan wasannin motsa jiki.

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

Ya alakanta karfin jikinsa da baiwar da Allah yayi masa inda aya bukaci tsofaffi da su dage da atisaye, duba lafiyarsu, cin abinci mai nagarta da kuma tattaunawa da jama'a domin samun tsufa mai kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel